Kitabı oku: «Wani Neman Jarumai », sayfa 10
SURA NA GOMA SHA BIYAR
Thor nata tafiya akan kodaden hanya mai dattin, da Reece, O’Connor, da Elden a gefegefensa. Dukansu hudu basu wani cewa juna komai ba tunda suka tashi, haryanzu akade. Thor ya kalli Reece da O’Connor dajin irin godiya agaresu da bai taba sani ba. Ya gagara yarda cewa zasu iya sakansu a hasari dominshi Kaman haka ba. Yaji cewa shi yasamu abokanen gaskiya, mafi kama yan’uwa. Baisan me loton kerike dashi musu ba, amma duk abinda zasu fuskanta, yayin farin cikin ganinsu a gefensa.
Yayita kokarin kar ya kalli Elden. Yanaganinsa yana buga duwatsu, yana rike da haushi, yana ganin yanayin haushi da tashin hankalinsa saboda kasancewarsa anan, a sintiri dasu. Amma Thor baiji tausayinsa ba. Kaman yadda Kolk yafada, shi yafara komai. Yayi masa kyau.
Dukansu hudu, taron hadi dabamdabam, sun cigaba da tafiya a hanya, suna bin kwatance. Sun dinga tafiya na sa’o’i, yammaci yayi, kuma kafafun Thor sun fara gajiya. Kuma yana jin yunwa. An bashi dan karamin kwano ne acike da miyan hatsi da rana sai yayi fatan susami abinci na jiransu a koma ina suka nufa.
Amma yanada damuwowinda suka fi wannan girma. Ya kalli rigar kariyarsa kuma yagane da baza a bashiba in babu dalili mai muhimmanci. Kafin a turosu, dukansu hudu anbasu kayan kariya na yangida: fata, da adon tsarka. An kuma basu guntayen takwafi na wani marakaifin karfe—ba Kaman na azurfanda ake baiwa gwanaye ba, amma yafi babu. Yaji karfin daya kasance da makami a kwankwasonsa—ahade, kuma, da majajjabarsa, wanda yake tafiyadashi haryanzu. Koda yake yasan inda zasu gamu da babban tashin hankali a daren yau, watakila makamanda akabasu su kasa tsaresu. Yaji kwadayin manyan makamain magabatansa a rundunan: madaidaita da dogayen takwufa, guntayen mashi, kulake, kananan wukake, gataru. Amma wadannan na yara masu suna da mutunci ne, daga sananun dangi, dazasu iya sayan irin wadannan abubuwan. Wannan kuma ba Thor bane, dan wani makiyayi kawai.
Ayayinda suka cigaba da gangarawa hanya marakarewa zuwa faduwan rana na biyu, nesa da mashigin fadan sarki mai maraba da kowa, zuwaga marabi mai nisa na loto, Thor yagagara jin cewa wannan duk laifinsa ne. Saboda wani dalili, wasu yan rundunan sunyi Kaman basua sonsa, Kaman sun kijinin kasancewansa. Abin bashida ma’ana. Kuma yana samasa mutuwan jiki. Duk rayuwansa abinda yaso kawai shine shiga cikinsu. Yanzu, yanaji Kaman yashiga ta bayan fage ne; yan’uwansa zasu taba yarda dashi kuwa?
Yanzu, akan komai, anwareshi domin zuwa sintiri a loto. Wannan ba adalci. Bashi yatayar da fadan ba, kuma da yayi amfani da baiwansa, koda sun zama mene, ba dagangan bane. Shima bai ganesu ba haryanzu, baisan daga ina suke zuwaba, baisan dayaya yake kiransuba, ko kuma yada zai kashesu. Bai kamata amasa horo saboda wannan ba.
Thor bashi da masaniyan abinda sintirin loto ke nufi, amma daga yanayin shauran, a fili yake, cewa ba abinso bane. Yayi tunanin ko anakaishi ne domin akasheshi, idan wannan ya zama hanyarsu naneman ya fita a rundunan na dole. Yanada muradin karya taba hakura.
“Yaya shauran nisan loton?” O’Connor ya tambaya, ya yanke shurun.
“Babu nisa sosai,” Elden ya amsa. “Da bamu shiga wannan damuwan ba inba domin Thor ba.”
“Kai katada fadan, katuna? Reece ya yanke masa Magana.
“Amma nayi fada mai safta, shikuma baiyiba,” Elden yakoka. “Ballema, yamasa kyau.”
“Sabodame?” Thor ya tanbaya, yana neman amsan tambayan daketa konashi taciki tun dazun. “Meyasa yamun kyau?”
“Domin baikamata kananan ba, damu. Ka saci masayinka a cikin runduna. Sharanmu zabanmu akayi. Kai da fada kashiga.”
“Amma ba dalilin rundunan kenan tun farko ba? Fada?” Reece ya amsa. “Zanyi musun cewa Thor nada alhakin wurinsa a ciki Kaman kowani dayanmu. Anzabemu ne kawai. Shi yayi gwagwarmaya da fada domin samun abinda ba a bashiba.”
Elden yakada kafada, darashin gamsuwa.
“Dokokin ne dokokin. Ba a zabeshi ba. Baikamata yakasance damu ba. Shiyasa nayi fada dashi.”
“To, bazaka sani na tafi nabari ba,” Thor yamayarda martini, muryarsa na girgiza, yanada muradin sai anyarda dashi.
“Zamu gani akan wannan,” Elden yayi gunaguni aduhunce.
“Kuma mekake nufi da wannan?” O’Connor ya tambaya.
Elden baisake badakai ba, amma yacigaba da tafiya cikin shuru. Cikin Thor ya murde. Yagagara kasa jin cewa yayi makiyya dayawa, kodayake baisan dalili ba. Baya son yanayin dayake jin.
“Kada ka wani kulawa dashi,” Reece yacewa Thor, yadaga murya domin shauran suji. Bakayi wani laifi ba. An turaka zuwa sintirin loto domin suna ganin yiwuwan abubuwa a jikinka. Anason a dafaka inbahaka ba da basu damuba. Kuma suna samaka ido saboda mahaifina yawareka. Shikenan.”
“Amma menene sintirin loto?” ya tambaya.
Reece ya gyara murya, ya damu.
“Ban taba zuwa ba nima. Amma naji labarai. Daga yara masu dan girman, dakuma daga yayuna. Aikin sintiri ne. Amma a daya gefen loto.”
“Daya gefen?” O’Connor ya tambaya, razana a muryarsa.
“Me kuke nufi da ‘daya gefen’?” Thor ya tambaya, darashin ganewa.
Reece ya karaneashi.
“Baka taba jin labarin loto bane?”
Thor najin shauran suna kallonsa, sai ya girgiza kai, dasaninsa.
“Kana wasa,” Elden ya harba.
“Haka?” O’Connor ya danna. “Ko sodaya a rayuwanka?”
Thor ya girgiza kai, launinsa ya canja. “Mahaifina baya taba kaimu ko’ina. Naji labarin.”
“Watakila bakataba fita daga kauyenku ba, yaro,” Elden yace. “Koka taba?”
Thor ya girgiza kafada, yayi shuru. Abin na nunawa sosai haka ne?
“Bai taba ba,” Elden yakara da rashin yarda. “Abin rashin yarda.”
“Ka rufe bakinka,” Reece yace. “Kafita hanyarsa. Wannan baisa kafishi da komai ba.”
Elden yayiwa Reece kallon rashinso yakai hanu kan gida takwafinsa, amma ya sake hanun. Daga gani, duk da yafi Reece girma, bayason ya tayarda hankalin dan sarkin.
“Loton ne kawai abinda kekare masarautarmu na zoben,” Reece yamasa bayani. “Babu wani abinda ke sakaninmu da shauran mutanen duniyan. Da mugayen dajujuka zasu ketareshi, da duk mun gama yawo. Zoban gabadaya nasa ido a kanmu, mayakan sarki, domin karesu. Munada yan sintiri suna tsaro a kowani lokaci—musamman a wannan gefen, daga lokaci zuwa lokaci kuma, a dayan. Gada daya ne kawai ya sallaka, hanya daya kawai na shiga ko fita, kuma mafi kwarewan yan Silver suna tsaro dare da rana.
Thor yaji labarin loton a gabadayan rayuwansa, yaji labarai na ban tsoro da mugayen abubuwanda ke boye a daya gefen, babban mugun masrautar dake kewaye da zoben, da kuma yaya kasancewansu kusa da abin tsoro. Yana daya daga cikin dalilansa nason yashiga rundunan sarki: yataimaka a kare danginsa da masarautarsa. Ya kijinin tunanin cewa akwai wasu maza a waje da suke kareshi alhalin shi yana zama rai akwance a cikin masarautar. Yaso yabada nashi gudumawan domin yakan tarin mugayen. Baya tunanin wani abin jaruntan dayafi wadannan mazan dake tsaron mashigin loton.
“Loton nada fadin mil daya, kuma ya kewaye duka zoben,” Reece yayi bayani. “Ketareshi bashida sauki. Amma ba mutanen mu kadai ne abinda ke hana taron shigowa ba. Akwai miliyoyin wadannan hallitun suna yawo, kuma idan sunso su haye loton, da karfin cin tuwo, zasu iya cikin dan lokaci. Karfin mutanen na taimakawa na makamashin loton ne kawai. Ainihin karfin dake hanasu shine karfin takwafin.
Thor yajuya. “Takwafin?”
Reece ya kalleshi.
“Takwafin Kaddara. Kasan tasuniyan?”
“Watakila wannan dan kauyen bai taba jin labarinsa ba,” Elden ya cusa.
“Lalle nasanshi,” Thor ya mayar,yana karekansa. Basaninsa kawai yayiba amma yayi kwanaki yana tunanin tasuniyan gabadayan rayuwarsa. Yana kwadayin yaga takwafin. Kirkiraren Takwafin Kaddaran, takwafin sihirin da makamashinsa ka kare zoben, mai cika loton da runduna maikarfin kare zoben daga masu kawo hari.
“Takwafin na zama a fadar sarki kenan?” Thor ya tambaya.
Reece ta amsa da kai.
“Yana zaune a cikin dangin sarauta tun iyaye da kakkanni. Arashinsa, masarautar bazata kasance komai ba. Zoben zata mamayu.”
“Idan muna da kariya, to menene dalilin sintirin loton kuma?” Thor ya tambaya.
“Takwafin na kare manyan barazanan ne kawai,” Reece yayi bayani. “Wani dan karamin masharantan halitta shi kadai na iya zamowa ciki nan da can. Dalilin bukatan mutanenmu kenan. Mutum daya na iya haye loton, kokuma dan karamin tawagansu—suna iya zama da rashin fargaban da zasu gwada haye gadan, kokuma buya su sauka daya gefen katangan loton su haura dayan. Aikinmu ne mutaresu. Koda halitta daya na iya barna dayawa. Shekarun baya can, daya ya zamo ciki ya kasha rabin yaran kauye daya kafin aka kamashi. Takwafin nayin mafi yawan aikin, amma muma bangare ne da baza a iya sharewa ba.
Thor yashigar dashi duka. Loton nada kamannin girma, aikinsu muhimmanci, yagagara yarda cewa shi zai kasance wani bangaren wannan babban burin.
“Amma duk da duka wannan, banyi bayaninsa sosai ba,” Reece yace. “Akwai Karin abubuwa akan loton fiye da wannan kawai.” Ya dawo yayi shuru.
Thor ya kalleshi sai yaga wani abu Kaman soro ko mamaki acikin idanunsa.
“Yaya zanyi bayaninsa nema?” Reece yace, yana kokarin samun kalmominda suka dace. Ya gyara murya. “Loton yafi dukanmu girma nesa ba kusaba. Loton ya…”
“Loton wurine na maza,” wani murya mai bada amsa ya zo.
Duk sun juya da zuwan muryan, da takun doki.
Idanun Thor sun waru. Isowa dadansauri daga gefensu, da adon cikaken tsarka, da dogayen makamai masu kyalli arataye a gefen hadadiyar dokinsa, sai ga Erec. Yayi murmushi zuwa garesu, da idanunsa akan Thor.
Thor ya kalli sama arikice.
“Wurine da zai mayar dakai namiji,” Erec ya kara. “Idan baka riga ka zama daya ba tukunna.”
Thor baiga Erec ba tun gasan, sai yaji Karin kwanciyan hankali da ganinsa, kasancewa da ainihin gwanin mayaki ayayinda suka nufi loton—kuma baragi ma, Erec dakansa. Thor yaji Karin karfi a kasancewa dashi, yayi fatan zai bisu.
“Mekakeyi anan?” Thor ya tambaya. “Zaka rakamu ne?” yatambaya, yana fatan banuna zalamansa ba.
Erec ya jinginu baya yayi dariya.
“Kada kadamu, dan yaro,” yace. “Zan biku ne.”
“Haka?” Reece ya tambaya.
“Al’ada ne wani dan Silver ya raka yan runduna ayayin sintirinsu na farko. Sai nabadakai.”
Erec yajuya sai ya kalli Thor a kasa.
“Tunda, kaima ka taimakeni jiya.”
Thor yaji zuciyarsa tayi dumi, yakarfafu da kasancewan Erec. Kuma yaji daguwa a idanun abokansa. Gashinan, yanasamun rakiyan gwarzon gwanin mayakin masarautar, ayayinda suka nufi loton. Mafi yawan tsoronsa yafara barinsa.
“Gaskiya, bazan fita sintiri daku ba,” Erec ya kara. “Amma zan jagoranceku a haye gadan, zuwa masuguninku. Aikinku ne ku fita sintiri, ku kadai, daga wurin.”
“Wannan babban darajawa ne, yallabai,” Reece yace.
“Mungode,” O’Connor da Elden suka hada murya.
Erec ya kaalli Thor a kasa yayi murmushi.
“Tunda ma, idan zaka zama dangidana na farko, bazan bari kamutu ayanzu ba.”
“Nafarko?” Thor ya tambaya, zuciyarsa na rasa bugu daya.
“Feithgold ya karya kafansa a gasan. Zai huta na akalla sati takwas. Kaine dangidana na farko ayanzu. Kuma horonmu nama iya faraway, ko bazai iya ba?”
“Na iyawa, yallabai,” Thor ya mayar da martini.
Zuciyan Thor nata yawo. Akaro na farko acikin dan lokaci, yaji Kaman sa’a yafara juyowa tagurinsa. Yanzu shine dangida na farko wa mafi hazakan duka gwanayen mayaka. Yaji Kaman shi yah aye dukan abokansa.
Dukansu biyar sun cigaba, sun nufi yammaci ta wurin ranar dake fadiwa, Erec na tafiya ahankali akan dokinsa a gefensu.
“Ina ganin Kaman kataba zuwa loton, yallabai?” Thor ya tambaya.
“Sau dayawa,” Erec yamayar. “Sintirina na farko. Ina daidai shekarunka, gaskiya.”
“Kuma yaya kasameshi?” Reece ya tambaya.
Duka yara hudun sun juya sai suka kalli Erec, cike da natsuwa. Erec yayi tafiya na wani dan lokaci a cikin shuru, yana kallon gabansa sambai, dashoshin sa a hade.
“Karon farko yakan kasance wanda mutum baya taba mantawa. Yanada wuyan bayani. Wani irin wuri ne sabo kuma awajen sanin mutum kuma da asiri da kuma kyau. Adaya gefen akwai hatsarori da hankali baya dauka. Gadan hayewan nada sawo dakuma tsayi. Akwai mu dayawa muna sintiri—amma a kullum, kanajin kai kadai ne. duniya ne a kololuwarsa. Yakan matse mutun domin yakasance a inuwarsa. Mutanenmu sunyi daruruwan shekaru suna sintirinsa. Gwajin hayewa ne. Baka ainihin gane ma’anar hatsari saidashi; bazaka iya zama gwanin mayaki ba saidashi.”
Yakoma yayi shuru. Yara hudun sun kalli juna, suna jin amai.
“Musammaci hayaniya a daya gefen kanan?” Thor ya tanbaya
Erec ya kada kafadarsa.
“Komai na iya faruwa, idan kuka kai dajujjukan. Dawuya. Amma maiyiwuwa.”
Erec ya kalli Thor a kasa.
“Kanason kazama jarumin dangida, kuma watarana, gwanin mayaki?” ya tambaya, yana kallon Thor sosai.
Bagun zuciyan Thor ya karu.
“Haka ne, yallabai, fiye da komai.”
“To akwai abubuwanda dole kakoya,” Erec yace. “Karfi kadai baya isa; zafin nama baya isa; zama gwarzon mafadaci baya isa. Akwai wani abu kuma, wani abinda yafi dukansu muhimmanci.”
Erec yakoma tasake shuru, kuma Thor yagagara kara jira.
“Menene?” Thor ya tambaya. “Menene yafi muhimmanci?”
“Dole ka kasance da ruhi mailafiya,” Erec ya amsa. “Tada kataba jin tsoro. Dole kashiga mafi duhun daji, mafi hatsarin yaki, da rashin haushi. Dole kadinga tafiya da wannan rashin haushin, akowani lokaci, kodayaushe kuma ako ina kaje. Bataba soro, kulum da kula. Bataba hutu, kulum aikin yakamata. Bakada zarafin jiran wasu su kareka kuma. Kai ba dankasa bane kuma. Yanzu kai dayane daga cikin mutanen sarki. Mafi girman yanayin jarumi karfin hali ne da rashin tsoro. Kada kaji tsoron hatsari. Amma kadaka nemeshi.
“Wannan zobenda muke zama cikinta,” Erec ya kara. “Masarautar mu. Kaman mu, da duk mutanenmu, muna kareshi daga taron mugayen duniya. Amma bamu kareshi. Loton ne take kare dukanmu, kuma da sihirinda ke cikinsa. Muna zama a cikin zoben maisihiri. Kadaka manta dahaka. Muna rayuwa mu mutu sa subbu. Babu kariya anan, yaro, akowani gefen loton. Ka dauke sihirin, ka dauke subbun, bamu da komai.”
Sun cigaba da tafiya acikin shuru na wani lokaci,ayayinda Thor le jujuya kalmomin Erec a zuciyarsa akai akai. Yaji Kaman Erec nabashi wata boyayyar sakone, Kaman yana gaya masa cewa, duk baiwanda yakedashi, kowane subbu yakekira, ba abin kunya bane. Alhali ma, abin alfahari ne, kuma wani tushin makamashi wa masarautar. Thor yaji sauki. Da yanajin Kaman ana turashi loton a masayin horone saboda amfani da baiwansa, kuma yana tsarguwa; amma yanzu yanajin baiawansa, koda sun kasance menene, zasu iya zama abin alfahari.
Yayinda shauran yaran suka ja gaba kuma Erec da Thor suka danyi baya, Erec ya kalleshi akasa.
“Kariga ka lallaba kayi wasu makiya masu karfi a fada,” yace, wani murmishi na fuskarsa. “Yawan makiya Kaman yawan abokanenka, yayi kamadahaka.”
Yanayin Thor ya canja, da kunya.
“Bansan tayaya ba, yallabai. Banyi niyan haka ba.”
“Ba a yin makiya da niya. Ayawanci lokuta akan yisu ne da hasada. Ka lallaba ka kirkiri dayawansa. Wannan bai zama lalle abu mara kyau ba. Ka zama dalilin ireiren ra’ayi.”
Thor yasosa kansa, yana kokarin yagane.
“Amma bansan dalili ba.”
Erec yayikamada abin na bashi dariya har yanzu.
“Sarauniya dakanta nakan gaba wurin gaaba dakai. Ka lallaba kakasance a gefenta mara daidai.”
“Mahaifiyana?” Reece ya tambaya, yajuya. Sabodame?”
“Wannan shine tambayan da yadameni nima,” Erec yace.
Thor yaji damuwa. Sarauniya? Abokiyar gaba? Menene yamata? Yagagara sani. Yaya za’ayi harshi yayi muhimmancinda zata sandashi? Baisan me ke faruwa akewaye dashi ba.
Bazato, wani abu yazo masa.
“Itane dalilin turoni nan? Zuwa loto? Ya tambaya.
Erec yajuya yakalli gabansa sambai, fuskarsa ya daina wasa.
“Zata iya zama,” yace, yana tunani. “Watakila ta iya zama.”
Thor yayi tunanin irin nisa da zurfin makiyan dashi yariga yasamu. Ya shiga fadanda baisan komai akai ba. Yaso ya kasance ne kawai. Yabi son ransa ne kawai, kuma yayi duk abinda zai iya domin cika burinsa. Bai taba tunanin cewa tayin hakan, zai iya tayarda hasada ka kishi ba. Yajujjuya shi a zuciyarsa, Kaman kacici kacici, amma yagagara kaiwa tushinsa.
Ayayinda Thor ke jujjuya wadanan tunanin, sun kai saman wani dan tudu, kuma yayinda kallon wajen ya shmfidu agabansu, tunanin komai ya zube. Numfashin Thor ma yatafi—kuma ba domin iska mai hurawa da karfin bane kowai.
Ashinfide agabansu, iyaganin ido, loton yake. Karo na farko kenan da Thor ke ganinsa, kuma kallon ya girgizashi har yakai ya daskare a wuri daya, yagagara motsi. Yakasance abu mafi girma da daukaka daya taba gani. Babban ramin cikin kasan yayi Kaman yamike har illa masha’a, ahaye da daya kawai, wato wani siririn gada ajere da mayaka. Gadan yayi Kaman shima yamike zuwa karshen kasa ne.
Loton na raye da launukan ganye da bula daga rana na biyu mai sauka, kuma haskensa mai kyalli na tasowa daga jikin katangunsa. Ayayinda yafara jin kafafunsa kuma, Thor yafara tafiya da shauran, kusa kusa da gadan, harsaida ya iya leka kasa, zuwa cikin zurfin duwatsun loton; sunyi Kaman sun gangara cikin hanjin kasa. Thor yama gagara gani kasan, kuma baisan ko hakadin yakasance domin bashidashi bane, kokuma domin gajimare sun rufeshi. Duwatsunda suka jeru sunyi kama da cewa shekarunsu sun kai miliyan, Kaman sun faru da yanayin da guguwa suka bari shekaru aru aru. Yakasance wuri mafi nisan tarihi dayataba gani. Bashi da sanin cewa duniyarsa nada girma haka, nada lafiya, nada rai.
Abin yayi Kaman yazo farkon hallita.
Thor yaji shauran sun ja numfashi akewaye dashi, suma.
Tunanin su hudu a sintirin wannan loton yayi kamada abin dariya. Sun wadantu daga ganima kawai.
Yayinda suka nufi gadan atafiye, mayaka sun bushe a kowani gefe, a attention, sun bada wuri wa sabbin yan sintirin. Thor yaji bugun zuciyarsa ta karu.
“Bana ganin yadda mu hudu zamu iya sintirin wannan,” O’Connor yace.
Elden yayi dariyan rainin wayo. “Akwai yan sintiri dayawa banda mu. Mu kawai hakori dayane a na’uran.”
Yayinda suke sallakagadan atafiye, karan da akeji kawai na iska mai huruwa ne, dana takalmansu, dana dokin Erec, shima yana tafiye. Kwofatonsa na barin wani kara mara komai amma mai karfafarwa, abinda kawai Thor ke iya kamawa a wannan bahagon wurin.
Bakodaya daga cikin mayakan, wadanda duk suka tsandare a gaban Erec, daya fadi koda kalma daya ayayinda suke sintiri. Maiyiwuwa sun wuce darurukansu.
Thro yagagara kin gani akowani gefensu, asoke akan kugiyoyi kowani dan taku kadan akan karfen gadan, akwai kan mugaye masu kawo hari. Wasu basu dadeba, suna digan jinni
Thor yakauda kai. Wannan yasa abin yazama zahiri. Baisan ko ashirye yake ma wannanba. Yayi kokarin kar tunanin yawan hargisin day a haifar da kawunan, rayukanda aka rasa, da kuma abinda ke jiransa a daya gefen, yayi damuwan ko zasu dawo. Wannan ne dalilin duka wannan saffaran? Domin akasheshi?
Ya leka kan gefen, zuwa marasa karewan bacewan duwatsu, sai yaji karan wani tsuntsu da nisa; yakasance karanda bai taba jib a. yayi tunanin ko wani irin tsuntsu ne, kuma wani ireiren dabbobi ne kuma ke makale a daya gefen.
Amma ba ainihin dabbobin ne suka dameshi ba, kokuma kawunan da aka soke. Fiye da komai, yanayinda yakeji a wurin ne. Yagagara gane ko domin raban ne, ko hurawan iska, ko girman budadiyar saman, kokuma hasken ranandake fadiwa—amma wani abu akan wannan wurin yakasance a bahagonce, yana sashi safara. Yana mamayeshi. Yanajin makamshin subbu mai nauyi na yawo akansu. Yayi tunanin ko kariyar takwafin ne, kokuma wani daddaden karfi. Yaji Kaman yana sallaka wani babban kasa, amma sallakawa zuwa wani duniyan rayuwa.
Kwanaki kadan da suka wuce kawai yakasance yana kiwon tumaki a karamin kauyensu. Yazama abin kasa yarda cewa ayanzu, akaro na farko arayuwansa, zai kasha dare, ba kariya, a daya gefen loton.
SURA NA GOMA SHA SHIDA
Ayayinda rana yafara bacewa daga sama—launin janbaki ahade dana bula dayayi Kaman yana mamaye duniyan—Thor na tafiya da Reece, O’Connor, da Elden suna gangarawa karamar hanyar dake shiga cikin dajin wajen. Thor bai taba kasancewa a dame haka ba arayuwnsa. Yanzu su hudun ne kawai, Erec yasaya a baya a masauki, duk da kokekokensu, Thor najin yanzun ne suke bukatan juna fiye da duk wani lokaci. Dole su hade da kansu, arashin Erec. Kafin su rabu, Erec yacemasu kada su damu, yace shi sai saya a masauki domin jin kiransu, kuma yakasance a wurinsu idan suna bukatansa.
Wannan na baiwa Thor dan karfin gwiwa ayanzu.
Ayayinda kaurin dajin ke raguwa akansu, Thor yakalli kewayen wannan wurin shakatawan, kasan dajin ajere da kayoyi da bakin ya’yan itace. Reshen bishiyoyi dayawa nada kullekulle kuma sun sufa, suna kusan taba juna, kusa da juna da sai Thor ya sunkuyar da kai. Sunada kayoyi amaimakon ganye kuma suna fita kota ina. Tsiro masu nannaduwa ajikin wasu masu lainin koyi sunratayu a wurare, sai Thor yayi kuskuren neman ya ture wani daga fuskarsa sai yagano ashe maciji ne. yayi ihu yayi tsalle yakauce a cikin dan lokaci ne.
Yayi sammanin shauran zasu masa dariya ne, amma su, suma, sun nisu da tsoro. Duka akewaye dasu akwai karan dabbobi iri iri. Wadansu karan kadan ne daga makogoro, wassu sosai suma huda wuri. Wasu suna zuwa daga nesa, wasu sunyi kusanda mutum zai damu. Duhun dare yazo da sauri ayayinda suka nufi zurfin cikin dajin. Thor yaji tabas ana iya samasu tarko a kowani lokaci. Ayayinda sama ke kara duhu, ganin fuskan yan’uwa nakara wuya. Ya kama marikan takwafinsa da karfinda sakiyan yasunsa sunyi fari, ayayinda dayan hanunsa ya kama majajjabarsa. Shauran sun kama makamansu, suma.
Thor ya umurci kansa da karfin zuciya, rashin shakka da karfin gwiwa kaman yadda gwanin mayaki mai kyau yakamata yakasance. Kamar yadda Erec ya umurceshi. Yafi masa ya fuskanci mutuwa a yanzu daya rayu kuln acikin soronta. Yayi kokarin daga habarsa yacigaba da tafiya gabagadi, harma da kara saurin tafiyan sa kuma yin gaban shauran da wasu taku.zuciyarsa nata bugawa, amma yaji Kaman yana fuskanyar su soronsa.
“Muna sintirin menene asali?” Thor ya tambaya.
Daga tambayan, sai yagane zai iya zama na wawanci, kuma yayi sammanin Elden yayimasa tsiya.
Amma ga mamakinsa, shuru ne kawai yaji. Thor yakalli baya yaga fararen idanun Elden, sai yagane yafishi jin soro. Wannan, akalla, yabaiwa Thor karfin gwiwa. Thor yafishi karacin shekaru da girman jiki, amma bai bar soro ya rinjayeshi ba.
“Abokan gaba, ina sammani,” Reece yace daga karshe.
“Kuma waye wannan?” Thor ya tambaya. “Yaya kamaninsa?”
“Akwai ireiren makiya dayawa anan,” Reece yace. Muna cikin waje ne yanzu. Akwai kasashen mugaye, da duka ireiren kabilu na mugayen hallitu.
“Amma menene manufan sintirin?” O’Connor ya tambaya. “Wani bambamci zamu iya yi da wannan? Idan ma muka iya kasha daya ko biyu, wannan zai dakatar da milyoyinda suke bayansa?”
“Bamu kasance ana domin mu magance komeba,” Reece ya amsa. “Mun kasance anan domin mu sanarda zuwanmune amadadin sarki. Domin susan kar suzo kusada loton dayawa.”
Ina ganin zaifi daidaida hankali mujira sai sunyi yunkurin ketareshi sai muyi maganinsu alokacin,” O’Connor yace.
“Babu,” Reece yace. “Yafi kyau ahansu nufannan. Dalilin wadannan sintirin kenan. Akalla, abinda yayana yace kenan.”
Zuciyan Thor nata bugawa yayinda suka cigaba da lumewa cikin zurfin dajin.
“Daidai wani nisa yakamata muyi?” Elden ya tambaya, yana Magana a karo na farko, muryarsa na rawa.
“Baka tuna abinda Kolk taceba?” sai mun ciro jan shaidan mu dawo dashi.” Reece yace. “wannan ne shaidan cewa munyi nisanda yakamata a sintirinmu.”
“Banga shaida ako inaba,” O’Connor yace. “Kai ma, banama ganin komai. Yaya yakamata mukoma?”
Babu wanda ya bada amsa.Thor na tunani Kaman haka. Yaya zasu iya ganin wani shaida a duhun dare? Ya fara damuwan ko wannan yaudara ne, wani yanayi aiki, wani daga cikin wasan kwakwalwa da yanrunduna keyi akan yara. Yayi tunanin kalmomin Erec kuma, yayi tunanin abokan gabansa masu yawa a fada. Yana da jin yanayi mara kyau akan wannan sintirin. Ko ana shirya masu gadar zare ne?
Bazato sai ga wani mumunan kara, biye da motsi acikin su reshe—sai wani babban abu yawuce gabansu aguje. Thor ya jawo takwafinsa, shauran ma haka, suma. Karan takwufa na barin jakukunansu, na karfe akan karfe, ya cika wuri yayunda duk suka saya a wuri, suna rike da takwufansu a gaba dasu,suna kallon soro zuwa lota ina.
“Menene wannan? Eledn yakoka, muryarsa na rawa da soro.
Dabban yasake wuce hanyarsu, yana gudu daga wani gefen dajin zuwa dayan, amma a yanzun sun masa kallo mai kyau.
Kafadun Thor sun sake daya gane dabban.
“Gada ne kawai,” yace, yasake sosai. “Gada sha bambam dana taba gani—amma gada dai duk da haka.”
Reece yayi dariya, karan karfafa gwiwa, dariyan dayafi shekarunsa girma. Da Thor yajishi, yagane dariyan sarkin watarana ne. Yaji Karin lafiya da abokinsa ke gefensa. Sai yayi dariya, shima. Dukan wannan soron don ba komai.
“Bantaba sanin cewa muryarka kan sinke inkaji soroba,” Reece yayiwa Elden tsiya, yasake fashewa da dariya.
“Inda zanganka, da zan nannausheka,” Elden yace.
“Ina ganinka da kyau,” Reece yace. “Zo ka gwada.”
Elden ya gware masa ido, amma bai isa yayi motsi ba. Maimakon haka, ya mayarda takwafinsa dakinshi, kamar yadda shauran sukayi. Thor yaso Reece saboda lasa Elden da yakeyi; elden yakan yiwa kowa tsiya—ya cancanci shima yasamu kadan. Yaso rashin soron Reece cikin yin hakan saboda alhali, Elden ya ninkashi a girma.
Daga karshe Thor yaji zafinkai yabar jikinsa kadan. Sun cikaronsu na farko, kankaran ya narke, kuma suna raye. Yayi baya yayi dariya, shima, yana farincikin kasancewa da rai.
“Kacigaba da dariya, bakon yaro,” Elden yace. “Zamuga waye zaiyi dariya daga karshe.”
Bana dariyanka, Kaman yadda Reece keyi,Thor yayi tunani. Ina jin sakewa dan ina raye ne kawai.
Amma baidamu yafada ba; yasan babu abinda shi zai fada da zai juya kiyyayarsa a wurin Elden.
“Ku gani!” O’Connor yayi ihu. “A can!”
Thor ya matse ido amma baya ganin abinda yake nunawa dayasa a duhun daren. Sai yaganshi: alamar rundunan, yana lilo daga su reshen.
Duk sun fara gudun ciroshi.
Elden yawuce shauran dagudu, yana turesu da garaje
“Tutar din nawane!” yayi ihu
“Ni nafara ganinsa!” O’Connor ma yayi ihu
“Amma ni zan fara ciroshi, kuma nine zan maido dashi!” Elden yasake ihu
Thor ya kumbura; yagagara yarda da abinda Elden ke aikatawa. Ya tuna abinda Kolk yace—cewa duk wanda ya kawo shaindan nada kyauta—sai yagano dalilin gudun Elden. Amma wannan ba dalili bane. Yakamata suzama kungiya guda ne, taro—ba kowa takaitakai ba. Ainihin yanayin Elden yafara fitowa—bawanda ya fita aguje acikin shauran, yayi kokarin kada shauran. Yasa Thor yakara kin jinin Elden.
Elden yawuce aguje bayan yadoke O’Connor da gwiwan hanu, kuma kafin shauran su dauki mataki, yayi gabadasu da taku masu yawa sai ya cafko shaidan.
Yayin yin hakan wata babbar raga tafito daga bako ina, tataso daga kasa, tayi tsalle zuwa sama cikin iska, ta kama Elden sai ta dagashi sama. Yana lilo gaba da baya agaban idanunsu, kafa daya kawai daga wurinsu, Kaman dabban da tarko ya kama.
“Ku taimakeni! Ku taimakeni!” yana ihu, asorace.
Duk sun rage tafiya yayinda suka yi kusa dashi; Reece yafara dariya.
“To, waye masoracin ayanzu? Reece yafada da karfi, abin yabashi dariya.
“Mene kai dan karamin kaguwa!” yayi ihu “Zan kasheka idan na sauko daga wannan!”
“Haka? Reece ya lasa. “Kuma ayaushe kenan?”
“Ku saukeni!” Elde na ihu, yana juyawa da wainuwa acikin ragan. “Na umurce ku!”
“Oho, ka umurcemu, ko bahakaba?” Reece yace, yafashe da dariya kuma. Reece yajuya yakalli Thor.
“Menene tunaninka?” Reece ya tambaya.
“Ina ganin cewa yanada bashin tubawa dukanmu,” O’Connor yace. “Mussamman Thor.”
“Nayarda,” Reece yace. “Zan gayamaka meza ayi,” yacewa Elden. “Kanemi gafara—kuma kasa yazama daga zuciyarka—sai na duba yankoka zuwa kasa.”
“Nabada hakuri?” Elden ya maimaita, asorace. “Ba a miliyan din rana ba.”
Reece yajuya zuwaga Thor.
“Watakila mubar wannan dunkulin anan yakwana. Zai zama abinci mai kyau wa dabbobin. Menene tunaninka?”
Thor yayi murmushi da fadi.
“Ina ganin tunanine mai kyau,” O’Connor yace.
“Kusaya!” Elden yayi kara.
O’connor ya mika hanu ya cafko alaman daga hanun Elden dake lilo.
“Ina ganin baka rigamu zuwaga alaman ba asali,” O’Connor yace.
Su ukun sun juya suka fara tafiya.
“Babu, kusaya!” Elden yakoka. “Bazaku barni anan ba! Bazaku ba!”
Dukansu ukun sun cigaba da tafiya.
“Ku gafarce ni!” Elden yafara kuka. “Kuyi hakuri! Ku gafarce ni!”
Thor yasaya, amma Reece da O’Connor sun cigaba da tafiya, daga karshe, Reece yajuya.
“Me kakeyi?” Reece ya tambayi Thor.
“Bazamu iya barinshi anan ba,” Thor yace. Duk da yadda Thor yakijinin Elden, baiyi tunani yayi daidai su barshi a wurin ba.
“Me zai hana?” Reece ya tambaya. “Shi yajawo wa kansa.”
“Inda dujine ta juyada mujiya, O’Connor yace, “Kaima kasan da farin ciki zai barka a gurin. Yaya zaka damu?”
“Nagane,” Thor yace. “Amma wannan baice muma mu aikata irin halinsa ba.
Reece ya daura hannayensa a kwankwasonsa sai yayi tsaki ayayinda yamaso yayi Magana a kunnen Thor.
“Dama bawai zan barshi awurin na daren gabadaya bane. Watakila rabin daren. Amma kana da huja. Bashida irin wannan zuciyan, watakila ciwon zuciya yakamashi. Kanada kirki dayawa. Wanna damuwa ne,” Reece yace yayinda yasa hanu akan kafadan Thor. “Amma dalilin da yasa nazabeka a matsayin aboki kenan.”
“Danima,” O’Connor yace, yasa hanunsa shima a daya kafadan Thor.
Thor yajuya, yataka zuwaga ragan, ya mika hanu, ya yankeshi zuwa kasa.
Elden yafado kasa da wani kara. Yatashi kan kafafunsa, ya wurgar da ragan, sai yadinga neman wani abu a kasa.
“Takwafina!” yayi ihu, “A ina yake?”
Thor ya duba kasa, amma duhu yayiyawa domin gani.
“Watakila shima yah aura cikin bishiyoyin yayinda ragan ta daga ka,” Thor ya amsa.
“Ko a ina yake, ya bata yanzu,” Reece yace. “Bazaka taba samunshi ba.”
“Amma baku ganeba,” Elden yaroka. “Rundunan. Doka dayane kawai. Kada kayadda kabar makaminka abaya. Bazan iya komawa babushi ba. Za a koreni!”