Kitabı oku: «Wani Neman Jarumai », sayfa 13

Yazı tipi:

“Ya isa!” yayi ihu.

Yaran sun dawo daga zagawansu suka fada kan ciyawa. Sun kwanta agurin, suna numfashi da sauri, suna kuma yi sama sama, suna cire rigan dole na tsarka da aka samusu. Thor, shima, ya zauna akan ciyawa, hannaye agajiye, yana digan gumi. Wasu mutanen sarki sun zagayo da bokatai na ruwa suka ajiye akan ciyawan. Reece ya mika hanu, ya dauko daya, yasha daga ciki, sanan ya mika wa O’Connor, wanda yasha sai ya mika wa Thor. Thor yasha yakuma sha, rowan na sauka habansa da kirji. Ruwan yayi dadi, yayi numfashi da karfi yayinda ya mayar wa Reece.

“Wani irin dadewa wannan zaiyi?” ya tambaya.

Reece ya kadakai, yana numfashi da karfi. “Ban sani ba.”

“Na rantse suna kokarin kashemu ne,” wani murya yazo. Thor yajuya yaga Elden, wanda yariga yazo yazauna a gefensa. Thor yayi mamakin ganinsa a wurin, sai yagane cewa dagaske Elden nason zama abokanai. Yazama shabambam ganin irin wannan sauyin a halinsa.

“Yara!” Kolk yayi ihu. Yana tafiya ahankali asakaninsu. “Mafiyawanku basua samun abinda suka auna ayanzu, a yammacin rana. Kamar yadda kuka gani, awu daidai yafi wahala idan ka gaji. Darasin kenan. Ayayin yaki, bazaka zama da rashin gajiya ba. Zaka gaji. Wasu yakin na iya daukan kwanaki. Tumbama idan kuna kaiwa fada hari. Kuma lokacinda kake agajiye ne yakamata dole kayi awunda ba kuskure. Yawancin lokaci zaka tilastu da wurga duk makamin da yasamu agareka. Dole kazama gwanin kowani makami, kuma akowani masayin gajiya. An gane wannan?”

“HAKANE YALLABAI!” suka mayar da ihu.

“Wassunku na iya wurga wuka, ko mashi. Amma wannan mutumin na rasa abinda ya auna idan yayi wurgi da guduma ko gatari. Kuna ganin zaku rayu da iya wurga makami daya kawai?”

“BABU YALLABAI!”

“Kuna tunanin wannan wasa ne?”

“BABU YALLABAI!”

Kolk ya juya yanayin fuska yayin tattakawa, yana buga yaranda yake ganin basu zauna amike bad a kafa a baya

“Hutunda kukayi ya isa,” yace. “Ku tashi!”

Thor ya lallaba yatashi da shauran, kafafunsa sun gaji, baisan irin wannan dazai iya jura kuma ba.

“Akwai bangare biyu a fadan nesa,” Kolk ya cigaba. “Kana iya wurgi—amma haka makiyinka ma. Intadauro bai siraba a rattan taku talatin—amma intadauro kaima baka sira ba, kamanshi. Dole ku yadda zaku kare kanku a rattan taku talatin. An gane wannan?”

“HAKANE YALLABAI!”

“Domin karekanka daga abin wurgi, baza bukaci lura da zafin nama akan kafafunka, domin tsunkuyawa, ko mirginawa, ko kaucewa kawai—amma kana bukatan gwaninta wurin kare kanka da babban kwangirin kariya.”

Kolk yayi nuni, sai wani mayaki ya kawo wata katuwar, kwagirin kariya mai nauyi. Thor yaji mamaki girman abin yakusan ninka nashi girman jiki.

“Zan samu mai badakai?” Kolk ya tambaya.

Taron yaran sunyi shuru, sunki badakai, sai batare da tunani ba, Thor, yasharo cikinlokaci daya, ya daga hanunsa.

Kolk yakada kai, sai Thor ya hanzarto zuwa gaba.

“Da kyau,” Kolk yace, “Ababu wawancin dayanku yakai na yabadakai. Inason muradinka, yaro. Matakin wawanci. Amma mai kyau.”

Thor ya fara tunani ko yadauki matakin wawanci dagaske yayinda Kolk yamika masa kwangirin kariyan karfen. Ya daura a hanu daya, kuma yagagara yarda da nauyinsa. Da kyar yake dagashi.

“Thor, burinka shine kayi gudu daga wannan karhsen filin zuwa dayan. Batare da kaji rauni ba. Kaga wadancan tara hamsin dake fuskantanka?” Kolk yace wa Thor. “duk zasu dinga wurga makamai zuwa gareka. Ainihin makamai. Ka gane wannan? Idan bakayi amfani da kwangirin kariyanka domin kare kanka ba, zaka iya matuwa kafin kakai daya gefen.”

Thor ya mayarda kallo cikin rashin yarda. Taron yaran sun dawo sunyi shuru.

‘Wannan bawasa bane,” Kolk yacigaba. “Wannan ainihi ne sosai. Yaki ainihi ne. raywa-da-mutuwa ne. ka tabbatta kanason badakai har yanzu?”

Thor yakada kai, adaskare dayawa cikin soro daya hanashi ce komai. Zaiyi wuya ya sauya ra’ayinsa a wannan lokacin, ba a gaban kowa ba.

“Da kyau.”

Kolk yayi nuni ga wani mai hidima, wanda ya maso gaba ya hura wani kaho.

“Kayi gudu!” Kolk yayi ihu.

Thor ya daga kwangirin kariya mai nauyin da hanu biyu, ya rikeshi da duk karfinsa. Yanayin hakan yaji wani kara, wanda karfinsa ya girgiza kashin kansa. Dole yazama guduman karfe. Bai huda kwangirin ba, amma yasamasa tsoro a duk jikinsa. Yayi kusan sake kwangirin, amma ta tilasta wa kansa rikeshi yacigaba da tafiya.

Thor yafara gudu, yana zilliya da duk irin saurinda ya iya da nauyin kwangirin. Ayayinda makamai da shauran abubuwanda aka wurgo ke wuceshi, ya tilasta wa kansa nannaduwa karkashin kwangirin kariyan iya iyawarsa. Kwangirin ne ceton ransa, kuma yana gudu, ya koyi yadda zai kasance akarkashinta.

Wani baka ya wuceshi, yarasashi da abinda baikai inci daya ba, sai yakara jan habarsa ciki. Wani abu mai nauyi yasake fadawa kan kwangirin, ya dokeshi dakarfinda ya mayar dashi baya wasu taku sai yafadi a kasa. Amma Thor yasake tashi yacigaba da gudu. Da babban kokari, yana numfashi sama sama, daga karshe ya sallaka filin.

“Ku saya!” Kolk yayi ihu.

Thor ya ajiye kwangirin kariyan, yana jike da gumi. Ya wuce godiya da yakai daya gefen; baisan ko zai iya rike kwangirin na wani dan Karin lokaci ba.

Thor ya hanzarta komawa ga shauran, yawancinda suka kalleshi da idon soyyaya. Yayi tunanin yaya kayi ya rayu.

“Aiki me kyau,” Reece yadan gaya masa a kunne.

“Akwai wassu masu badakai?” Kolk ya kira.

Sakanin yaran yayi shuru gabadaya. Bayan kallon Thor, bawanda yaso yasake gwadawa.

Thor yaji shi yayi abin bajinta. Baisani koda zai badakai dayasan abinda ya kunsa, amma yanzu yariga yawuce, yayi farin cikin shi yabadakai din.

“Yayi kyau. To ni zan badakai muku,” Kolk yayi ihu. “Kai! Saden! Yayi kira, yana nuna wani.

Wani mafi shekarun, siririn yaro yatako gaba, yakuma ji tsoro.

“Ni?” Saden yace, muryarsa na rawa.

Shauran yaran sunyi masa dariya.

“Waye. Banda kai?” Kolk yace.

“Yi hakuri, yallabai, zanfison kar na gwada.”

Wani irin jan numfashin tsoro ya taso asakanin yan rundunan.

Kolk ya nufeshi, hakora agwaye.

“Baka yin abinda gadama,” Kolk yamasa ihu. “Kana yin abinda nace maka kayi.”

Sadden yasaya adaskare, yanaji tsoro har mutuwa.

“Bai kamata yana nan ba,” Reece ya dan gayawa Thor a kunne.

Thor yajuyo ya kalleshi. “Me kake nufi?”

“Ya fito dangi masu masayi, kuma sun sasu anan. Amma baya son kasancewa anan. Ba mafadaci bane. Kolk yasan da haka. Inaganin sunason su dannashi ne. Inaganin sunaso yafita anan.

“Kayi hakuri, yallabai, amma bazan iya ba,” Saden yace, maganarsa na nuna tsoro.

“Zaka iya,” Kolk ya masa ihu, “kuma zaka yi!”

Ansamu wani daskararen, yanayin fuskantan juna.

Sadden ya kalli kasa, ya rataya habarsa a cikin kunya,

“Kayi hakuri, yallabai. Kabana wani aikin, sai nayi cikin farin ciki.”

Yanayin fuskan Kolk ya sauya, ya tattaki kasa ya nufeshi har sanda sakanin fuskokinsu baifi yan incina kadan ba.

“Zan baka wani aikin, yaro. Badamuwa na bane su waye danginka. Daga yanzu, zaka dinga gudu. Zaka dinga kewaye filin nan da gudu har sai ka fadi. Kuma bazaka dawo ba har sai kabadakai cewa zaka dauki wannan kwangirin kariyan. Ka fahimce ni?”

Sadden yayi Kaman zai fashe da kuka, yayinda ya kada kai a bada amsa.

Wani mayaki yazo, yasanya sarkan karfen kan kafadan Saden, sai wani mayakin ya kara na biyu a kansa. Thor yagagara gane yadda zai juri nauyin su ba, dakyar yake gudu da guda daya ma.

Kolk ya kwanta baya sai ya harbi sadden da kafa da kuma karfi a duwawu, sai ta tafi gaba yana tangal tangal sai ya fara doguwar, gudun a hankalinsa na kewaye filin. Thor yajimasa rashin dadi. Ayayinda yake kallonsa yana tafiya dakyar, yagagara fasa tunanin ko yaron zai rayu a rundunan.

Babu zato wani busa yayi kara, sai thor yajuya yaga wasu mutanen sarki haurowa akan dawakai, wurin yan Silver goma sha biyu na tare dasu, suna rike da dogayen mashi suna kuma sanye da hulunan karfe masu gashin tsunsu. Sun saya a gaban yan rundunan.

“Domin karama ranan auren diyar sarki, da kuma karama sakiyan rani, sarki ya nada shauran yau a ranan farauta!”

Duka yaranda ke kewaye da Thor sun ballada ihu. Gaba daya, suka shiga wasewa aguje, suna bin dawakai din yayinda suka juya suka ruga a sallaka filin.

“Me yake faruwa?” Thor ya tambayi Reece, yayin fara gudu da shauran.

Reece yasa babban murmushi a fuskarsa.

“Wannan aikekeniyan Allah ne!” yace. “Mun kamala a yau! Yakamata muje farauta!”

SURA NA ASHIRIN DA DAYA

Thor ya gangara hanyan dajin tareda shauran aguje kadan kadan, yana rike da mashinda aka bashi domin farautan. Agefensa akwai Reece, O’Connor da Elden, tare da akalla wasu yan runduna hamsin. Agabansu yan Silver dari ke haure, kan dawakai da kananan kayan karuya, wasu na rike da guntayen mashi, amma yawanci da kwari dab aka arataye akan bayansu. Da gudu asakinsu kuma akwai dozin dozin na yangida da masu hidima.

Akan doki agaba akwai sarki MacGil, da girmansa da jida kansa kamar yadda aka saba, wani murmushin farin ciki a fuskarsa. Ya kasance da yaransa Kendrick da Gareth agefensa, kuma, Thor yayi mamakin ganin har, Godfrey. Dozin dozin nay an kore nata gudu asakaninsu, wassunsu na kwaciya baya suna hura busanda akayi daga harwan giwa; wasu suna jan karnuka masu haushi, wadanda suka dan kara gudu zuwa gaba domin lamo dawakai din. Yanayin yazama gabadaya hayaniya ne. ayayinda babban taron ta tashi shiga dajin, sun fara rarrabuwa ta ko ina, kuma Thor baisan inda zasu je ba, kokuma wani kungiyan zai bi.

Erec na tafiya a kurkusa, sai Thor da shauran suka yanke shawaran bin hanyarsa. Thor yayi gudu zuwa gefen Reece.

“Ina zamu je?” ya tambayi Reece, yana numfashi da kyar yayin gudun.

“Can cikin zurfin dajin,” Reece ya mayar da kira. “Mutanen sarki na fatan dawowa da naman farauta da zai kai kwanaki.”

“Yaya wasu yan Silver ke kan dawakai alhali wasu suna kafa?” O’Connor ya tambayi Reece.

“Nakan dawakan na harin dabbobinda basu da wuyan farauta, Kaman barewa da fakara,” Reece ya mayar. “Suna amfani da kwarinsu. Wadanda ke kafa na harin dabbobinda suka fi hatsari. Kaman alade mai bindi mai rowan kwai.

Thor najin farin ciki da tsoro dajin ankira sunan daban. Yataba ganin daya lokacinda yake girma; dabba ne mai hatsarin gaske, sannane da iya yaga mutum biyu daga an dan bashi haushi.

“Daddadun jarumai kan kasance kan dawakai saisu bi barewa da tsunsaye,’ Erec yakara, yana kallon kasa. “Yaran kan kasance a tafiye a kafa, kuma subi manyan dabbobi. Sai kanada koshin lafiya ka iya, dama.”

“Wanda shine dalilin dayasa muka yardar da wannan farautan ma ku yara,” Kolk, yana gudu da shauran a kusa, yayio ihu, “horo ne muku, kuma. Zaku kasanca a kafa gabadayan farautan, kuma tafi daidai da dawakai din. Muna tafiya, zaku kasu zuwa kananan kungiyoyi, kuma kowani kungiya ta juya nata hanyan, sai kowanne ta farauci nata dabban. Zaku samu dabba mafi masifanda zaku iya samu—kuma zaku yi fadadashi har mutuwansa. Wadannan ne irin jaruntanda suke mayar daku mayaka: juriya, rashin tsoro, da kuma rashin shan kayen abokin gabanku, komin girma da muguntansa. Yanzu kuje!” yayi ihu.

Thor yakara gudu, Kaman dukan yan’uwansa, suna gudun kamo dawakai din yayinda suke rugawa cikin dajin yagagara sanin ina zaibi, amma yayi tunanin yasaya kusa da Reece da O’Connor, bazai samu matsala ba.

“Wani baka, da sauri!” Erec yayi ihu zuwa kasa.Thor ya ruga aiki, yana gudu a gefen dokin Erec, yakamo baka daga jakan gefen sirdin, sai ya mika masa. Erec ya kafu akan kwafrinsa yayin sukuwa, yarage tafiya, yayi awu mai kyau ga wani abu a cikin dajin.

“Karnukan!” Erec yayi ihu.

Daya daga cikin masu hidiman sarki ya saki kare mai haushi, wanda ya ruga cikin dajin. Ga mamakin Thor, wani babban tsunsu ya wuce, sai yayin wucewan, Erec yasaki bakan.

Harbin yayi daidai, yashiga wuyan daidai, sai tsunsun ya fadi, amace. Thor yayi mamakin yadda Erec yaganta.

“Tsunsun!” Erec yayiwo ihu.

Thor yayi gudu, ya dauko macecen tsunsun, dadumi, jinni na zbowa daga wuyarsa, sai ya koma ga Erec aguje. Ya kilaceshi akan sirdin Erec domin yayita lilo awurin yayin sukuwansa.

Gabadaya akewaye da Thor, dayawan gwanayen mayaka nata yin haka, suna koro tsunsaye kuma suna harbesu wa yangida su dauko. Yawanci suna amfani dab aka; wasu suna amfani da mashi. Kendrick ya janyo mashinsa baya, yayi awu, awurgashi ga wata barewa. Harbin yayi daidai, yawuce makogoronta daidai, kuma tafadi, itama.

Thor yayi mamakin yawan namomin daji a wannan dajin, irin yawan dukiyanda zasu dawo gida dashi. Zai isa ciyar da fadan sarki na kwanaki.

“Kataba kasancewa a farautan da ne?” Thor yayiwo kira ga Reece, ya kaucewa dannuwa awurin wani mutumin sarki dad an kadan ayayinda suke gudu. Jin wuri yayi wuya, da haushin karnuka, karan busa, da ihun mutane, suna dariya, sunyi nasara, yayinda suke ta kayarda dabba bayan dabba.

Reece nada babban murumushi a fuskansa yayinda ya salaka wata bishiya a kwance ya cigaba da gudu.

“Sau dayawa! Amma saboda mahaifina ne kawai. Basu bari mushiga farautan sai munkai wasu shekaru. Abune na nishadi—koda take Kaman babu wadda ke fita acikinsa babu rauni. Fiye da mutum daya yaji ciwo, ka yamutu, yanabin aladen daji.

Reece na numfashi sama sama yayin gudu. “Amma nakan hau bayan doki ne,” ya kara. “Ba a taba barina a kafa ba, tare da runduna, taba farautan aladen daji ba. Nafarko ne gareni!”

Babu zato dajin ta sauya, da dozin dozin din hanyoyi ashimfida agabansu, kowane yarabu zuwa hanyoyi dozin. Wani busan yayi kara, sai baban kungiyan ta fara rarrabuwa zuwa kananan kungiyoyi.

Thor ya makale kusa da Erec, sai Reece da O’Connor suka samesu; sun juya zuwa wata karamar hanya daya juya sosai zuwa kasa. Sunyi gudu kan gudu, Thor narike da mashinsa da karfi yayin salaka wata fadama. Karakar tawagansu ya kunshi Erec da Kendrick akan dawakai, Thor, Reece da Elden a kafa wada yamaidasu shida—da Thor ya juya, ya gano wasu yan runduna biyu suna haurowa abayansu, suka hadu dasu. Suna da girma da fadi, da gashi amurmurde daya sauka kasa da idanunsu, da manyan murmushi. Sunyi Kaman sun girmi Thor day an shekaru—kuma tagwaye ne.

“Nine Conval,” daya yayi kira zuwaga Thor.

“Nine Conven.”

“Mu yan’uwa ne,” Conval yace.

“Tagwaye!” Conven ya kara.

‘Ina fatan bazaku damuba idan muka hadu daku,” Conval ya gaya wa Thor.

Thor yakan gansu a runduna, amma bai taba haduwa dasu ba. Yayi murnan haduwa da sabibbin yan runduna, tunbama wadanda ke zuwa da abokantaka ba masa.

“Munyi murnana kasancewa daku,” Thor yayiwo kira.

“Idan hanaye suka yiyawa yafi kyau,” Reece yace.

“Naji aladun dajin wannan dajin nada girma,” Conval yace.

“Kuma suna iya kisa,” Conven ya kara.

Thor ya kalli dogayen mashinda tagwayen ke dauke dasu, sayinsu ya ninka nashi sau uku, sai yayi tunani. Ya kula cewa suna kallon nashi guntun mashin.

“sayin wannan mashin zai kasa,” Conval yace.

“Wadannan aladundajin nada kahon giwa. Kana bukatan abinda yafi tsayi,” Conven yace.

“Ka karbi nawa,” Elden yace, yayi gudu zuwaga Thor ya mika masa mashinshi.

“Bazan karbi naka ba,” Thor yace “Me kai zaka yi amfani dashi?”

Elden yakada kafada. “Zan kasance babu damuwa.”

Thor yaji da kirkinsa, sai yayi mamakin yadda abokantakarsu ta sauya a yanzu.

Ka dauki daya acikin su nawa,” wani murya yabada umurni.

Thor yadaga ido yaga Erec yazo gefensa, yana nuna sirdinsa, wanda ke dauke da dogayen mashi guda biyu.

Thor ya mika hanu sai ya ciro doguwar mashi daga sirdin, yana godiyan samunsa. Yafi nauyi kuma gudu dashi yafi wahala—amma yaji shi yanada Karin kariya, kuma abin na kamada zai bukaceshi.

Sun yi gudu akan gudu, har saida isak yafara konewa a cikin huhun Thor kuma baisani ko zai iya kara yin gaba ba. Ya kasance da lura, yana kallon kewayensa ko da alaman wani naman daji. Yaji yanada kariya da wadannan mutanen a kewaye dashi, kuma bazai tabuba da doguwar mashin. Amma yakasance da rashin kwanciyae hankali kuma. Bai taba farautan aladen daji ba. Kuma bashi da masaniyan abinda yakamata ya jira.

Yayinda huhunsa ke konewa, dajin ya budu zuwa wani dan shararen fili kuma abin godiya, Erec da Kendrick sun sayarda dawakansu. Thor ya dauka wannan ya basu izinin su saya, suma. Duk sun saya a wurin, dukansu takwas a shararen wurin, yaran a kafa suna mayarda numfashi, kuma Erec da Kendrick sun sauko daga dawakansu. Dawakan ma na numfashi sama sama, amma banda wannan ko ina yayi shuru, sautinda akeji kawai shine na iska acikin bishiyoyi. Karan daruruwan mutanen dake dajin yanzu yadauke, sai Thor yagane dole sunyi nisa da shauran.

Ya kalli kewayen shararen wurin, yana numfashi dakyar.

“Banga wani alaman dabbobi ba,” Thor yacewa Reece. “Kokai kagani?”

Reece ya girgiza kai.

“Aladen daji dabba ne mai dabara,” Erec yace, yatako zuwa gaba. “Bazai cika nuna kansa ba. Wani lokacin shi yake kasancewa yana kallonka. Zai iya jira sai baka zato, sai yataso. Ku dinga lura akowani lokaci.”

“Hankali!” O’Connor yayi ihu.

Thor yajuya sai babu zato wani babban dabba ya ballo cikin shararen wurin da babban hayaniya; Thor yadan jadabaya, yanaganin Kaman wata aladen daji ne ke kawo musu hari. O’Connor yayi ihu, sai Reece yajuya ya wurga masa mashi. Baisameshi ba, sai dabban yatashi sama. A lokacin ne Thor yagane cewa tolotolo ne kawai, yabace cikin dajin kuma.

Duk sunyi dariya, hankaliya kwanta. Yanayin O’Connor ya sauya, sai Reece ya aza masa hanun kwantar da hankali akan kafadarsa.

“Kada ka damu, aboki,” yace.

O’Connor ya kauda fuska, yaji kunya.

“Babu aladun daji anan,” Elden yace. “Munzabi hanya mara kyau. Abinda ke wannan hanyan kawai tsunsaye ne. zamu dawo hanu-safai.”

Watakila wannan ba abu mara kyau bane,” Conval yace. “Naji fadan aladen daji kan zama komutuwa- korai.”

Kendrick ya kalli dajin a nitse; Erec ma haka. Thor nagani a fuskan wadannan mutane biyun cewa akwai wani abu a dajin. Yana iya ganewa daga gwanintansu da hikima cewa sun kama kura sosai.

“To. Kaman hanyan yakare anan,” Reece yace. “ sabodahaka idan muka cigaba, dajin bazai zama da alama ba. Bazamu iya dawowa ba.”

“Amma idan muka koma, farautanmu yakare, O’Connor yace.

“Menene zai faru idan muka koma hanu-safai?” Thor ya tanbaya. “Babu aladen daji?”

“Zamu zama abin dariyan shauran,” Elden yace.

“A’A’ bazamu zama ba,” Reece yace. “Ba kowa ne yake samun aladen daji ba. Kai, samun daya ma yafi rashin samu wahala.”

Yayinda tawagan su ka saye a wurin shuru, suna numfashi sama sama, suna kallon dajin, Thor bazato ya gano shi yasha ruwa dayawa. Yanata rikewa duk tsahon farautan kuma yanzu jakan fitsarinsa nata zafi, yagagara daurewa.

“Ku dan ban wani dan lokaci,” yace, yafara kama hanyarsa na shiga dajin.

“Ina zakaje?” Erec ya tambaya, da kula.

“Dole ne nadan rage. Zan dawo yanzu.

“Kada kayi nisa,” Erec ya gargadeshi.

Thor, da lura, ya hanzarta zuwa cikin dajin sai yaje kwatancen taku ishirin daga shauran, sanda yasamu wuri da baza a gansa ba.

Daidai yana gama ragewa, bazato, yaji motsin reshen karamin itace, kara nada dama kuma babu wai, kuma yasani—yasanine kawai—wannan ba daga mutum bane.

Yajuya ahankali, gashin bayan wuyansa sun tashi, ya leka. Can agaba, watakila Kaman taku goma, akwai wani dan shararen fili kuma, wani dan karamin dutse a sakiyarsa. Sai a wurin, a kasan dutsen, akwai motsi. Wani karamin dabba, bazai iya cewa ko menene ba.

Thor yayi waswasin ko yakoma ga mutanensa kokuma yaga menene a wurin. Babu tunani, yayi rarrafe zuwa gaba. Koda wani irin dabbane, baiso ya rasa shi ba, kuma idan yakoma, watakila yariga yatafi kafin shi yadawo.

Thor ya dada masawa kusa, gahinsa atashe yayinda dajin keta kara kauri kuma sararin motsi keta raguwa. Baya ganin komai illa massasun bishiyoyi, rana kuma na haskawa a kwance dayawa. Daga karshe yakai shararen wurin. Yayinda ya nufo, ya sake kamunsa akan mashin, ya sauko dashi zuwa kugunsa. Yayi mamaki da abinda yagani agabansa cikin shararen wurin, a cikin dan inda hasken rana yake.

Awurin, yana motsi a ciyawan gefen dutsen, akwai yaron damisa. Yazauna a wurin yana motsi da kuka, yana kifta ido a rana. Yayi Kaman yanzu aka haifeshi, kusan sayinsa taku daya, kankantarsa yakai nay a iya shiga rigan Thor.

Thor yasaya awurin, yana mamaki. Yaron damisa farine kota ina, kuma yasan dole yaron farin damisa ne, mafi karacin samuwan duk dabbobi.

Daya ji wani karan ganye na bazata abayansa, yajuya yaga tawagan gabadaya sun nufeshi aruge, Reece a gaba, yana nuna damuwa. Cikin dan lokaci, sunkai kansa.

“Kaje ina ne?” ya tambaya. “Mun dauka ko kamutu.”

Yayinda suka iso gefensa suka kuma gad an damisan, yajisu suna numfashi dakyar saboda mamaki.

“Alama mai muhimmanci,” Erec yacewa Thor. “Ka samu abin samun rayuwa gaba daya. Mafi rashin samuwan dabbobi. Anbarshi shi kadai. Bashida mai kula dashi. Wannan na nufin yazama naka. Hakinka ne ka raineshi.”

“Nawa?” Thor ya tambaya, arikice.

“Hakkinka ne,” Kendrick ya kara. “Kaika sameshi. Ko, kuma nace, yasame ka.”

Thor ya rikice. Yayi kiwon tumaki, amma bai taba renon dabba ba arayuwansa, kuma bashi da sanin abinda yakamata yayi.

Amma kuma a lokaci guda, yariga yaji dangantaka mai karfi da wannan dabban. Kananan, idanunsa masu launin bula sun budu kuma sunyi Kaman shi kadai suke kallo.

Ya nufeshi, asunkuye, ya daukeshi a hanunsa. Dabban ya dago sama ya lashe kumatunsa.

“Yaya mutum yake rainon dan damisa?” Thor ya tambaya, yana mamaki.

“Ina gani yadda mutum yake kula da komai ma,” Erec yace. “Ka ciyar dashi yayinda yake jin yunwa.”

“Kaidai bashi suna,” Kendrick yace.

Hor yayi tunani ahankali, yana mamakin wannan ne karonsa na biyu dazai baiwa dabba suna acikin kwanaki biyu. Yatuna wata labara daga yarantansa, akan wata zakinda ta dami wani kauye.

“Krohn,” Thor yace.

Shauran sun kada kai na yarda.

“Kaman tasuniyan,” Reece yace.

“Inason sunan,” O’Connor yace.

“Krohn zai kasance,” Erec yace.

Yayinda Krohn yasauke kansa zuwa kirjin Thor, Thor yaji Karin karfin haderwarsa dashi fiye da duk wani abinda yataba mallaka. Yagagara daina jin Kaman yasan Krohn a rayuwowi yayinda dabbar ke masa motsi da kara.

Babu zato wani sananen kara yazo, wanda yatayar da gashin bayan wuyan Thor, kuma yasashi juyawa ya kalli sama da sauri.

A can sama, saiga Estopheles. Ya sauko kasa kasa kwassam, yanufi kan Thor, yana kara yayin hakan, kafin ya daga adakika na karshe.

Yayinda Thor ke tunanin ko yana kishin Krohn ne. Amma kuwa, da rattan dakika daya kawai, Thor ya gane: hankakarsa na masa gargadi ne.

Jim kadan wani sannanen kara yataso daga daya gefen dajin. Karan ganye ne, abiye da tasowa—kuma yafaru da sauri mai yawa.

Saboda gargadin, Thor nada babban sa a—yaganshi zuwa sai yayi sale ya kauce da rattan dakika daya, yayinda wata babbar aladen daji ta taso masa sambai. Ya kuskureshi da misalign gashi kwaya daya.

Shararen wurin ya balla cikin hayaniya. Aladen yataso ma wasu, sosai, yana wurga kahonsa kota ina. A wurgi daya ya lallaba ya kirci hanun O’Connor, sai jin yafara zuba yayinda ya rike wurin, yana ihu.

Abin yayi kamada kokarin fada damuturu, amma batare da makaman da suka kamata ba. Elden yayi kokarin soka masa doguwar mashinsa, amma aladen ya juyo kansa ne kawai, ya riko mashin da babban bakinsa, kuma a mataki daya mai safta ya rabata biyu. Sai aladen yajuya yataso wa Elden, ya doke masa hakarkari; sa’an Elden, ya sira daga aladen ya keketashi da kahon sa dadan rata karami.

Sun gagara dakatar da aladen. Yanason shan jinni, kuma tabbattace bazai barsuba sai yasamu.

Shauran sun hadakai suka fara aiki. Erec da Kendrick sun zaro takwufansu, hakama Thor, Reece da shauran.

Duk sun kewaye dabban, amma nada wuyan duka, tunba saboda kahonsa mai sayin taku uku wanda yahanasu zuwa kusa das hi. Yana kewayawa a guje, yana binsu a kewayen shararen filin. Yayinda suke daukan hanuhanu a kai hari, Erec yasamu nasran samu daidai awu, ya yankashi daga gefe; amma wannan aladen watakila anyioshi daga karfe ne, saboda ya cigaba da tafiya ne kawai.

A wannan lokacin komai ya sauya. Na wani dan lokaci, wani abu ya kama kallon Thor, sai yajuya yakalli cikin dajin. A can dad an nisa, aboye abayan bishiyoyi, da zai rantse yaga wani mutum da bakar, mayafi mai hula; yaganshi na daga kwari da baka yakuma auni sakiyan shararen filin. Kaman ba aladen yake aunawa ba amma mutanen.

Thor yayi tunanin ko yana mafarki ne. Zai iya zama an kawo masu hari ne? Anan? A sakiyan bako ina? Kuma daga waye harin?

Thor yabar tunaninsa ya rigayya. Yaji cewa shauran na cikin hatsari, sai ruga masu. Yaga mutumin na auna Kendrick da kwarinsa.

Thor yayi sale zuwaga Kendrick. Ya tureshi dakyau, yakatae dashi akasa, kuma yanayin hakan, jim kadan bakan yawuce, shauran kadan yasameshi.

Nan da nan Thor yasake kallon dajin, yana neman alamun mai kawo harin. Amma ya tafi.

Amma bashi da lokacin tunani; aladen nata sale sallen hauka har yanzu a filin, taku daya kawai daga wurinsu. Yanzu yajuya zuwa ta wurinsu, kuma Thor bashi da lokacin mayar da martini. Ya shirya kansa wa faruwan yayinda dogaye, kuma masu kaifin kahon giwa suka sauko kansa sambai.

Jim kadan wani irin kara yazo; Thor yajuya yaga Erec na dale bayan dabban, yadaga takwafinsa sama da dukanin hanayensa, sai ya soka cikin bayan wuyan wuyarsa. Dabban yayi ihu, jinni na zubowa daga bakinsa yayinda ya nadu a gwiwa, sai yafadi akasa, Erec a samansa.yasaya daidai taku daya ne kawai daha Thor.

Kowa yasaya adaskare a wuri daya, suna kallon juna—suna mamakin menene yafaru yanzu a doron kasa.

Yaş sınırı:
16+
Litres'teki yayın tarihi:
10 ekim 2019
Hacim:
292 s. 5 illüstrasyon
ISBN:
9781632912473
İndirme biçimi:
Serideki Birinci kitap "A Jeren Zoben Mai Sihiri"
Serinin tüm kitapları
Metin
Ortalama puan 5, 1 oylamaya göre
Metin
Ortalama puan 4,8, 6 oylamaya göre
Metin
Ortalama puan 5, 1 oylamaya göre
Metin
Ortalama puan 4,8, 5 oylamaya göre
Metin
Ortalama puan 5, 2 oylamaya göre
Metin
Ortalama puan 0, 0 oylamaya göre
Metin
Ortalama puan 0, 0 oylamaya göre
Metin
Ortalama puan 0, 0 oylamaya göre
Metin
Ortalama puan 0, 0 oylamaya göre
Metin
Ortalama puan 0, 0 oylamaya göre