Kitabı oku: «Wani Neman Jarumai », sayfa 2
“Kai karami ne, yaro. Kana da zuciyan maza. Amma ba a shirye kake ba. Ka dawo ka samemu in an yayeka.”
Da waanan, sai ya juya ya ruga, bama kallon shauran yara mazan. Ya hau dokinsa a gagauce.
Thor, rai a bace, ya kalli tayarwan tawagan; Kaman yadda suka iso da sauri, suka tafi.
Abu na karshe da Thor yagani shine yan’uwansa, azaune a bayan rumfan amalanken karshe, suna kallonsa, da rashin aminci, suna masa dariya. Ana tafiya dasu a gaban idonsa, nesa daganan, zuwaga rayuwa mafi inganci.
Daga cikin zuciyarsa, Thor yaji Kaman yamutu.
Da hayaniyan da ya kewaya shi ya kare a hankali, duk mutanen kauyen su sun kokkoma gidajensu.
“Kasan irin wawancinda kanuna, wawan yaro?’ mahaifinsa ya haura, ya kuma cafke kafadunsa. “Kasan da zaka iya bata wa yan’uwanka sa’ansu da zarafinsu?”
Thor ya ture hannayen mahaifinsa daga jikinsa da haushi, sai mahaifin ya miko hanu ya mari fuskansa da bayan hanu.
Thor ya ji zafin abin ya mayar da hararo ga mahaifinsa. Wani bangarensa, a karo na farko, yaso ya rama marin da mahaifin ya masa. Amma ya kama kansa.
“Je ka dawo da garken tumakina. Yanzu! Kuma in ka dawo, karka sa ran zan ciyar da kai. Za ka rasa abincin daren yau, sai kayi tunani a kan abinda ka aikata.”
“Watakila bazan ma dawo ba gaba daya!” Thor na ihu yana juyawa don ya tafi, ya bar gida, ya nufi su tudun bayan gari.
“Thor!” mahaifinsa ya kira da karfi. Yan kalilan din kauyawan da suka rage a kan hanya sun saya suna kallo.
Thor ya fara shi ba gudu ba shi kuma ba tafiya ba, sai ya fara gudu, yanason ya nisanci wannan gurin gwargwadon abinda ya samu. Baima san shi ya fara kuka ba, hawaye sun mamaye fuskarsa, yayin da duk mafarkun da ya taba rike wa a zuciyarsa suka cikaro da mummunan mutuwa.
SURA NA BIYU
Thor yayita yawo a cikin daji na sa’oi, cike da fushi, kafin daga karshe ya zabi wata yar tudu ya zauna, hannayensa a nade a kan kafafuwansa, yana kallon sararin Allah. Ya kalli bacewan amalankun, yayita kallon kuranda suka tayar na wasu sa’oi bayan su sun bace.
Bazasu sake kawo wata ziyara ba. Yanzu ya kamu da kaddaran zaman kauyen nan na shekaru kenan, yana jiran wata zarafin – idon ma sun dawo kenan. In kuma mahaifinsa ma ya yarda kenan. Yanzu zai zama shi da mahaifinsa, su kadai a gida, kuma tabattace mahaifinsa zai huce haushinsa a kanshi. Zai cigaba da kasancewa bawan mahafinsa, shekaru zasu yita tafiya, sai shima ya karasa rayuwansa Kaman nashi, a makale da dan karamin rayuwa, na leburanci – alhali yan’uwansa sunsamu yabo da sanuwa. Jininsa nata tafasa da rashin ji dakai a kan lamarin duka. Ba wannan rayuwan yakeso ba. Kuma shi ya san da haka.
Thor yacigaba da wasa kwakwalwa ko akwai abinda shi zai iya yi, ko ta wani hanya domin ya juya lamarin. Amma babu komai. Kaman haka kaddara da rayuwa ya rubuta masa zai kasance.
Bayan zaman sa’oi, ya tashi ba karfin gwiwa, ya fara komawa saman sananen tudun, Karin hawa akan Karin hawa. Bamusu, ya koma zuwaga garken, zuwa ga tudu mai tsayin. Yayinda yake haurawa, rana ta fadi a sama kuma na biyun ta kai kololuwa, ta sa yanayi mai rowan ganye a kan wuri. Thor ya dauki lokacinsa, a yayinda ya dinga tafiyan a hankali, ya ciro majajjabarsa daga kugunsa, fatan marikan a kode saboda shekarun datayi ana amfani da ita. Ya shiga cikin buhun da shima ke kugunsa ya tabo zabbabun duwasunshi, kowanne yafi mabiye dashi taushi, zabbabu daga mafi kyawun koramu. Wani lokacin yakan harbi tsunsaye; a wassu lokutan kuma, beraye. Wannan hali ne da ya sabar ma kansa a cikin shekaru. Da farko, baya samun abinda ya harba; saikuma, a lokaci daya, ya harbi abu mai tafiya. Tun daga lokacin saitinsa ya tabbata. Yanzu, wurga duwatsu ya zama masa jiki – kuma ya taimaka masa wurin huce haushi. Yan’uwansa suna iya sara itace da takwafinsu – amma bazasu iya harbin tsuntsun da ke tafiye da dutse ba.
Thor yasa dutse a majajjabar Kaman ba komaiba, ya dan kwanta baya, sai ya harba da dukan karfinsa, da tunanin Kaman yana wurgin mahaifinsa ne. Wurgin yasamu wani reshe a kan wata bishiya da nisa, ya kuma sauke shi farat daya. Tunde ya gano cewa shi yana iya kashe dabbabobi da suke tafiya, ya daina aunasu, yana tsoron baiwansa kuma bayason yaji ma komai ciwo; yanzun reshen bishiyoyi ne abun aunawansa. Saidai, in har, dila ya biyo garkensa. A cikin lokaci, suma sun koyi kiyayewa, sai tumakin Thor a sabili dahaka, su kafi nakowa sira a kauyen.
Thor yayi tunanin yan’uwansa, yayi tunanin inda suke a yanzu, sai ya fara taffasa. Bayan tafiyan wuni zasu isa haraban sarki. Yana ganin hoton hakan a zuciyarsa. Yana ganin isowansu ga babban buki, mutane a kayayyaki mafi kyau, suna gaishesu. Jarumai suna gaishesu. Yan Silver. Za a shigardasu, a basu wurin zama a barikin rundunan, wurin koyo a filin sarki da mafi kyawun makamai. Kowanne za a lakaba masa sunan wani sananen bafaje. Wata rana kuma, suma zasu zama fadawa, a basu dawakai, tambarin kare kasa da nasu mallakaken fili. Zasu kasance cikinsu bikibiki na kowane shekara suna kuma ci suna sha tare da sarki. Wannan rayuwa mai dadi ne. Kuma duk wannan ya zame masa.
Thor ya fara ji Kaman bayi da lafiya, sai ya nemi ture dukkan wannan tunanin daga zuciyarsa. Amma ya gagara. Wani bangaren jikinshi, bangare mai zurfi, dayake masa ihu. Yana ce masa kar ya fidda sammani, cewa yana da babban kaddara daya fi wannan. Baisan me kaddarar ba, amma yasan ba a nan take ba. Yana jin shi daban ne. Watakila ma na musamman. Kuma duk sun raina masa isa.
Thor ya kai dan tudu mafi sayi sai ha hango garkensa. Masu ladabi, haryanzu a tare, suna more kowane ciyayi suka samu da gamsuwa. Ya kirgasu, yana duba jan alamu dashi yayi a kan bayan kowanne. Jikin shi ya mutu daga gamawa. Tumaki daya ya bata.
Ya sake kirgasu, ya kuma sakewa. Ya gagara yarda: guda daya ya kauce.
Thor bai taba batar da tumaki ba, kuma mahaifinsa bazai taba barinshi araye ba saboda wannan. Abu mafi muni kuma, shi dakansa ya ki jinin tumakinsa ya bata, shi kadai a daji, komai ma na iya faruwa dashi. Ya kijinin yaga abunda bai san hawaba balle sauka yana shan wuya.
Thor ya hanzarta zuwa saman tudun ya duddubi kota ina har sanda ya hange tumakin, a can da nisa, gaba da wasu tudun: makadaicin tumakin, jan alaman a kan bayansa. Shine mai rigiman cikinsu. Gabansa ya fadi da gano cewa ba gudu kadai tumakin yayiba, amma inda ya zaba, a cikin duk wuraren duniyan nan, ya nufa shine yamma, zuwa Darkwood.
Thor ya hadiye yawu. Darkwood ya haramta – ba wa tumaki kadaiba, har wa mutane. Yafi karfin sanin kauyen, kuma tunda ya fara tafiya, Thor ya san ba a zuwa wurin. Bai taba ma gwada haka ba. Zuwa wurin, a fadin tarihi, tabbatacen mutuwa ne, bishiyoyin ba a tsare wa kuma cike da munanan namomin daji.
Thor ya kalli saman da ta fara duhu, yana kwokwanto. Bazai iya barin tumakin ya tafi ba. Yayi lissafin cewa inshi ya hanzarta, zai iya dawowa dashi a kan lokaci.
Bayan wegen baya na karshe, ya juya yafara dan gudu, ya nufi yamma, zuwaga Darkwood, hadiri ya kuma hadu a sama sosai. Yana jin mutuwan jiki, amma kafafuwansa suna ta tafiyar dashi. Ya ji cewa ba komawa da baya a yanzu, koda shi yaso hakan.
Wannan yayi daidai da gudu zuwa shiga mafarki.
*
Thor ya gangara jerin su tudun a guje ba hutawa, zuwa cikin kakauran inuwar Darkwood. Karamin hanyan takawan ya kare ne a inda dajin ya fara, sai ya shiga inda bata da tsari a guje, bushasun ganye suna kara a karkashin takunsa.
Daga shigarsa cikin bishyoyin duhu ya rufeshi, dogayen bishiyoyin cediyan sun toshe haske daga sama. Cikin nan yafi sanyi, kuma, yana ketare iyaka, ya ji sanyin ya rabeshi. Ba daga duhun kadai bane, ko daga sanyin – daga wani abu ne dabam. Abinda bazai iya baiwa suna ba. Wani yanayine…..na Kaman wani na kallonsa.
Thor ya daga ido ya kalli su reshen bishoyoyin da kyau, amumurde, har sun fishi kauri, suna laiyi suna kara a iskan da yake dan hurawa. Daga daukan kwatankwacin taku hamsin a dajin sai ya fara jin karan dabbobi wanda ba a saba ji ba. Ya juya amma baya ma ganin hanyar da ya shigo ta ita; ya riga ya fara jin Kaman babu hanyan fita. Sai yayi waswasi.
Darkwood ya kasance baya tunanin mutanen garin kuma baya tunanin Thor, wani abu mai zurfi mai kuma al’ajabi. Duk makiyayin da ya taba batar da tumaki zuwaga dajin bai taba tunanin ya bishiba. Har mahaifinsa. Labarain wannan gurin na da mumunan duhu, mumunan naciya.
Amma akwai wani abu da ya sha bambam a wannan ranan da yasa Thor ya ki ya damu, daya sa shi ya gagara takasamsam. Wani zuciyansa nason yayi abinda bai taba yi ba, ya nisanci gida gwargwadon iko, ya kuma bar rayuwa ta kaishi duk inda taga ya dace.
Ya dan kara lumewa, sai ya saurara, bashi da tabbacin ina yakamata yabi. Ya gano wasu alamu, lankwasasun reshe da suke nuna hanyar da watakila tumakinsa yabi, sai ya juya ta wurin. Bayan dan wani lokaci ya sake wani juyawan.
Kafin wani sa’an ya wuce, yayi mumunan bata. Yayi kokari tuno ta inda ya biyo – amma bashi da tabbaci. Wani irin rashin ganewa ya cika masa ciki, amma sai yaga mafita kawai zai kasance ta gaba ne, sai ya cigaba da tafiya.
Daga dan nesa can, Thor ya hango wani dan haske, sai ya nufeshi. Ya since kansa a wani dan shararen fili, sai ya saya a karshensa, yadaskare – abinda ya gani ya kasance abin babban mamaki.
A saye a wurin, da bayanshi a juye zuwaga Thor, sanye da doguwar riga, kuma mai launin bula, wani mutum. Kai, bama mutum bane – Thor najin haka daga inda ya saya. Wannan wani abu ne dabam. Sheihin wani addini, watakila. Yana da sayi kuma a mike yake, ya rufe kai da hulan alkebba, ba ko motsi, Kaman bashi da ko damuwa a duniyan nan.
Thor ya rasa mai zaiyi. Yakanji labarin wadannan shehunai, amma bai taba karo da ko daya ba. Daga alamun da ke kan doguwar rigarsa, da gol dinda ya kewaye bakin rigan, wannan ba shaihin malamin addini bane kawai: alamun nan na sarauta ne. Na fadar sarki. Thor ya gagara fahimtan abinda ke tafiya. Menene shaihin adini daga fada yake yi a nan?
Bayan lokaci mai tsawo, shaihinya juyo a hankali ya fuskance shi, daga yin haka, Thor ya gano fuskan. Hakan yaso ya dauke masa numfashi. Fuskan na cikin wadanda a kafisani a masarautan gaba daya: shaihin sarki dakansa. Argon mai bawa sarakunan masrautar yamma shawara tun shekaru aru aru.
Abinda yakeyi a nan, wuri mai nisa haka daga fada, a sakiyan Darkwood, ya kasance sirri. Thor nama tunanin ko mafarki shi yakeyine.
“Iddanunka basu rudeka ba,” Argon yace, yana kallon Thor kai saye.
Muryarsa tayi zurfi, irin nadaa, Kaman bishiyoyin dakansu ne sukayi Magana. Manyan idanuwansa, masu kama da leda sunkamanci huda jikin Thor, suna aunashi. Thor yaji wani abu Kaman makamashi na tashi daga jikin shaihin – Kaman yana saye a daya bangaren rana.
Thor ya sauka kan gwiwowinsa ya suguna da kai a sunkuye.
“Mai martaba,” yace. “Ka gafarce ni domin na dameka.”
Yiwa mashawarcin sarki wulakanci zai iya jawo tsari a kurkuku koma mutuwa. Wannan zahirin ya riga ya kafu a zuciyan Thor tunda a ka haifeshi.
“Tashi ka mike, yaro,” inji Argon. “Da naso ka durkusane, ai dana gaya maka.”
Ahankali, Thor ya tashi ya kalleshi. Argon yayi wasu taku ya matso kusa. Ya saya ya kurewa Thor kallo, har sanda Thor yaji abin yadameshi.
“Kadauki idanun uwarka,” Argon yace.
Sai Thor ya tuna baya. Bai taba haduwa da mahafiyarsa ba, kuma bai taba haduwa da kowaba, banda mahaifinsa, wanda yasanta. An bashi labarin ta rasu a wurin aihuwa, wani abinda Thor yakejin cewa laifinshi ne. Tunda yana jin Kaman shi yasa iyalansa suka tsaneshi.
“Ina ganin Kaman kana daukana a matsayin wani daban ne,” Thor yace. “Bani da uwa.”
“Baka da uwa?” Argon ya tambaya yana murmushi. “Namiji kadai ne ya aifeka?”
“Ina nufin ince ne yallabai, mahaifiyana ta rasu a haihuwa. Ina ganin kana kuskuren sanina ne.
“Kaine Thorgrin, na dangin McLeod. Dan autan yara maza hudu. Wanda ba a zaba ba.”
Idanun Thor sun budu da fadi. Yarasa yaya zai fassara wanan lamarin. A ce mutum mai matsayin Argon yasan shi waye – wanan ya fi karfin fahimtansa. Bai taba tunanin an sanshi a wajen kauyensuba.
“Yaya……kasan duk wannan?”
Argon ya mayar da murmushi, amma baiyi Magana ba.
Kwasam sai Thor ya ciku da jin son sani.
“Ta yaya…” Thor ya kara, yana neman kalmomin da zaiyi anfanidasu, ….ta yaya ka wayi mahaifiya na? ka taba haduwa da ita ne? Wacece ita?
Sai Argon ya juya yayi tafiyarsa.
“Tambayoyin wani lokaci nan gaba,” yace.
Thor ya kalli tafiyarsa, arikice. Wannan ya zame masa haduwa mai rikitarwa da al’ajabi, kuma nata faruwa da sauri. Ya ga baikamata ya bar Argon yatafi haka kawaiba; ya bishi da sauri.
“Me kakeyi anan?” Thor ya tambaya, yana saurin ya kamo shi a tafiya. Argon, da sandan girmansa, irin na daa da akayi daga ivory, nata tafiya da sauri. “Bani kake jira ba dama ba, ko ni kake jira?’
“In ba kai ba sai waye?” Argon ya tambaya.
Thor na sauri domin ya kamoshi, yanabinshi sunata shiga dajin, sun bar shareren sararin a baya.
“Amma yaya saini? Yaya kasan zan kasance anan? Mai kakeso?”
“Tambayoyi dayawa,” Argon yace. “Kana chika iska da Magana, ka kasa kunne a madadin haka.”
Thor nata binshi a yayin da suka yita dada lume kurmin dajin, yana iya karfinsa domin yin shuru.
“Kazo neman tunkiyanka data bata,” Argon yace. “Kokari maikyau. Amma bata lokaci. Bazata rayu ba.”
Idanu Thor sun budu da fadi.
“Tayaya kasan wannan?”
“Nasan su duniyan da bazaka taba saniba, yaro. Koda zakasansu, ba yanzuba.”
Thor yayi mamaki yayin da ya kara saurin tafiya domin kamoshi.
“Bazaka kasa kunneba, kodashike. Haka yanayinka. Taurin kai. Kaman mahaifiyarka. Zaka cigaba daneman tumakinka, da muradin cetonta.”
Thor ya girgizu a yayin da Argon yayita fadan abubuwan da ke cikin tunaninsa.
“Kai yarone mai bin abinda ranka ke so,” ya kara. “Taurin-hali. Ji dakai. Yanayi nagari. Amma wata rana zai iya zama dalilin fadowanka.”
Argon ya fara haurawa wani dan kunya mai ciyayi, kuma Thor na biye dashi.
“Kanason ka shiga rudunan sarki,” Argon yace.
“Kwarai!” Thor yabada ansa, da faraha. “Akwai wani daman a yiyuwar haka a gareni? Zaka iyasa hakan ya faru?”
Sai Argon yayi dariya, kara mai zurfi, kuma mara komai ciki daya haura har kashin bayan Thor.
“Zan iya sa komai yafaru kuma bazan iya sakomai yafaruba. An riga an rubuta kaddararka. Ya raga nakane ka zabeshi.”
Thor bai gane ba.
Sun kai saman kunyan, inda Argon ya saya yakuma fuskanceshi. Thor na saye kusadashi, sai makamshin Argon yabi jikinsa.
“Kaddararka ta kasance mai muhimmanci,” yace. “Kada ka gujeta.”
Idanun Thor sun kara buduwa. Kaddararsa? Muhimmanci? Yaji kanshi nata kumbura.
“Ban ganeba. Kana mani Magana a habaince. Yi hakuri, ka kara mini bayani.”
Sai Argon ya bace.
Bakin Thor ya kara buduwa domin mamaki. Yayi kallo zuwaga ko ina, yana kasa kunne, yana mamaki. Ko duk a tunaninsa ne kawai? Ko wani irin mafarkine?
Thor ya juya ya kalli dajin da kyau; daga wannan guri mai kyau, a can samman kunyan, yana kallo da nisa fiye da dazun. A yayinda yake kallo, ya hango wani motsi a gaba kadan. Yaji kara kuma yayi zaton tumakinsa ne.
Sai ya fara gagautawa a gangarwa kunya mai cayayin yana sauri zuwa ta inda yaji karan, daga baya ta cikin dajin. Yana tafiya amma yana tuna haduwansu da Argon. Yayimasa wuya ya yadda da abinda ya auku a sakaninsu. Menene mai bawa sarki shawara keyi anan, a cikin duk wurare? Kuma yakasance yana jiran zuwansa ne. Amma domin me? Kuma me ya nufa da kaddararsa?
Duk sa’ilin da Thor yayi kokarin kara fahimtan wannan lamarin, sai kara rashin fahimta yakesamu. Argon ya masa gargadin kar yaci gaba a yayinda da kuma ya kwadaitar masa da yin hakan kuma ta wata hanyar. A yannzu, yanakan tafiya, Thor natajin wani Karin yanayin haramci, Kaman wani muhimmin abu na shirin faruwa.
Ya shiga wani kwana sai ya saya a tsandare saboda abinda yakegani a gabansa. Farat daya duka munanan mafarkinsa suka tabbatu. Gasusuwan jikinsa sun mike a tsaye, sai ya fahimci cewa shiga Darkwood dinsa yakasance babban kuskure.
A dayan gefenshi, kwatankwacin taku talatin kawai, sai ga wata dabbar Sybold. Yana kumburi, a mumurde, a tsaye a kan kafafunta hudu, kusan girman doki, ya kasance dabban da a ka fi tsoro a Dakrwood, watakila ma a masarautar. Thor bai taba gani ba, amma yaji tasuniyoyin. Yana kama da zaki, amma yafi grima, fadi, fatansa jajazur kuma idanunsa launin kwai mai kyalli. Tasuniya na nuna cewa yasamo jan fatansa ne daga jinin yaranda basuciba basuganiba.
Thor zai iya kirga iya lokutan da yaji labarin anga wannan babban dabban a gabadaya rayuwansa, duk da ana ganin wadansuma karya sukeyi. Watakila wannan ya kasance ne domin babu wanda ya taba karo da wannan daban ya tsira. Wasu na ganin dabban Sybold shine sarkin dajujjuka, kuma Kaman wani alaman karfanci. Komenene karfanci, Thor bai saniba.
Ya ja baya da taku daya amma da kulawa.
Dabban Sybold din, da hakora a kwaye, dogayen hakoran sakiyan bakinsa na digarda yawu, na mayar masa da harara da idanunsa masu launin kwai. Yanada battacen tumakin Thor a bakinsa: yana ihu, yana rataye kai a kasa, rabin jikinsa a hude da dogayen hakoran. Yana kusa da mutuwa. Daban Sybold din na jin dadin kamun dayayi, yana daukan lokacinsa; Kaman yana jin dadin bama tunkiyan azaba.
Thor ya gagara sayawa yana jin kukan. Tumakin yayita motsi gefe da gefe, ba maitaimako, sai yaji yakamata shi yayi wani abu.
Tunanin Thor na farko ya gudu ne, amma ya riga yasan haka zai zama a banzane. Wannan mumunan daban yafi komame gudu. Idon shi yagudu zai karawa dabban karfin gwiwa ne kawai. Kuma bazaya bar tumakinsa ya mutu haka kawai ba.
Ya saya a daskare da tsoro, kuma ya san dole shi yayi wani abu kada ma menene.
Bazatarsa ya rinjayeshi. Yasa hanu a hankali a cikin jakarsa, ya ciro kwayan dutse daya, ya sashi a majajjaba. Da hanu yana girgiza, ya waina, ya dauki taku daya zuwa gaba, sai ya wurga.
Dutsen yayi tafiya a iska yaje ya samu abunda ya auna. Harbi daidai. Ya samu tumakin a cikin kwayar idonsa, yawuce sambai zuwa kwakwalwarsa.
Tumakin ya kwanta shuru. Amace. Thor ya kawo karshen wahalarsa.
Dabban Sybold din ya gwaye idanunsa, yaji haushin Thor ya kashe abin wasansa. Ahankali ya bude manyan hakoransa ya sake tinkiyan, wanda ya fado da kara a kan kasan dajin. Sanan ya sanya hankalinsa a kan Thor.
Yayi ihun barazana, mummunan kara mai zurfi, daya taso daga can cikin tumbinsa.
Yayinda ya fara taku zuwa gareshi, Thor, zuciyarsa na bugu, ya daura wani dutsen a majajjabarsa, ya masa baya, da shirin yin wani harbin.
Dabban Sybold din ya fita a guje, yana gudun da yafi duk abinda Thor ya taba gani a rayuwarsa.
Thor yayi taku daya zuwa gaba sai ya harbor dutsen, yana adu’an Allah yasa yasameshi, domin yasan shi bazaya samu wata zarafin yin wani harbinba kafin ya iso.
Dutsen yasamu mummunan daban a idonsa na gefen dama, ya kuma cire idon. Wurgin ya kasance mai kyau sosai, wanda zai iya kayarda dabba inda karama ce.
Amma wannan ba karamin dabba bane. Mummunan daban ya gagara taruwa. Ya kara ihu daga cutuwan, amma bai ko rage guduba. Duk da rashin ido daya, duk da dutsen a makale a kwakwalwarsa, ya chigaba da nufan Thor da yaki. Ba abinda shi kuma Thor zai iyayi.
Jim kadan, mummunan daban na kansa. Ya waina manyan faratun kafansa ya yakushi kafadarsa.
Thor yayi ihu. Abin yayi kamada wukake uku suna yankamasa naman jikinsa, jinni mai zafi yana bulbulowa daga mikin.
Mummunan daban ya dannashi a kasa, a kan hannaye da kafafuwa. Yanada shegen nauyi, Kaman wata giwa ne a saye akan kirjinsa. Thor yaji kasusuwan kirjinsa suna wargazuwa.
Mummunan dabban ya dan ja kansa baya, ya bude bakinsa da fadi yananuna dogayen hakoran sakiyansa, ya fara saukowa dasu zuwaga makogoron Thor.
Yanakan hakan, Thor ya mika hannayensa ya cafko wuyan; daidai yake da riko jijiyar karfe. Da kyar Thor ya jura. Hannayensa suka fara girgiza a yayinda dogayen hakoran suka fara kara saukowa. Yaji numfashin dabban dazafinshi a duk fuskarsa, yaji yawun dabban na gangarawa wuyarsa. Wani irin kara ya taso daga can cikin kirjin dabban, yana kone kunnuwan Thor. Yasan shi zai mutu.
Sai Thor ya rufe idanunsa yana adu’a.
Kayi hakuri, Allah.ka bani karfi. Ka yarda mani nayi fada da wannan halittan. Kayi hakuri. Na rokeka. Zani yi duk abinda kace nayi. Zan ci bashinka mai yawa.
Sai kawai wani abu ya faru. Thor yaji wani zafi na musamman yataso daga cikin jikinsa, yana bin hanyoyin jininsa, Kaman wani filin makamashi dayake gudu a cikin jikinsa. Ya bude idnunsa sai yaga abin mamaki: daga hannayensa wani haske mai launin kwai na fita, a yayinda yake ture makogoron mummunan dabban, damamaki, ya iya kamanta karfin dabban ya tareshi danisa.
Thor ya cigaba da turi har saida ya fara ture mummunan dabban. Karfinshi ya cigaba da karuwa har yaji wani dunkulalen karfi – daga bisani kadan, mummunan dabban ya wurgu zuwa ta baya, Thor ya tureshi har kafa goma masu kyau. Ya fada akan bayansa.
Thor ya taso zuwaga zama, bai fahimci abinda ya faru ba ko kadan.
Dabban ya sake tashi. Sanan, a cikin haushi, yasake tasowa – amma a wannan lokacin Thor najin dabam. Karfin na ratsan dukanin jikinsa; yana jin karfin da bai taba ji ba.
A yayinda dabban yayi tsalle sama, Thor ya dan durkusa kasa, ya cafkoshi ta cikinsa, sai ya wurgar dashi, yasa nauyinsa ya daukeshi.
Dabban ya tafi a sama a cikin dajin, ya pasu da bishiya, sanan ya fado was a kasa.
Thor ya ware idanu, yana mamaki. Yanzu shi ya wurgarda dabban Sybold kenan?
Mummunan dabban ya kyafta ido sau biyu, sai ya kalli Thor. Ya tashi ya rugo kuma.
Wannan karon, yayinda dabban ya kawo hari, Thor ya cafkoshi a makogoro. Dukkansu zun zuba a kasa, dabban a saman Thor. Amma Thor ya juya ya koma saman dabban. Thor ya rikeshi, yana matse wuyarsa da hannayensa duka biyu, yayinda shi kuma dabban keta kokarin daga kai ya cijeshi da dogayen hakoransa. Bai sameshi ba. Thor, da jin wani karfi, ya dada danna hannayensa batare da yasake ba. Ya bar karfin ya ratsi jikinsa. Sai jim kadan, da mamaki, yaji karfinsa yafara fin na mummunan dabban.
Yana shake dabban Sybold din zuwaga mutuwa. Daga karshe, mummunan daban ya saki jiki.
Thor yaki ya sake har na wani cikakken minti daya.
Ya tashi a hankali, da kasawan numfashi, yana kallon kasa, idanu a ware, yayin da ya rike hannunsa daya ji ciwo. Menene ya faru yanzu? Wato shi, Thor, ya kashe dabban Sybold kenan?
Ya jicewa wannan alama ne, a wannan ranan ranakun. Yaji Kaman wani muhimmin abu ya faru yanzu. Yanzuyanzu shi ya kashe dabba mafi sanuwa kuma wanda a kafi tsoro a duk wanan masarautar. Shi-kadai. Batare da wani makami ba. Kaman ba da gaske bane. Babu wanda zai yadda da labarinsa
Yanajin duniyan na kewayawa ayayinda yake tunanin wani irin karfi ne yashigeshi, abinda wannan yake nufi, asalin mutumim dashi ya kasance. Mutanen da aka sansu da irin wannan karfin su Druid ne kawai. Amma kuma ai mahaifinsa da mahaifiyarsa basu kasance Druid ba, saboda haka bazai yiwu shi ya zama daya ba.
Ko kuma zai iya zama ne?
Dayaji Kaman da mutum a bayansa, Thor ya juyo yaga Argon a tsaye a wurin, yana kallon dabban a kasa.
“Da yaya kazonan?” Thor ya tambaya, yana mamaki.
Argon yayi Kaman bai jishiba.
“Ka shaidi abinda ya faru?” Thor ya tambaya, har yanzu bai yarda ba. “Ban san yanda na aikatashi ba.”
“Amma kasani,” Argon ya ansa.”A can ciki, kasani. Kai daban ne da duka shauran.”
“Yayi kama da…..muhimmin Karin karfi,” Thor yace. “Kaman karfinda nima bansan inadashiba.
“Kewayen makamashin,” inji Argon. “Watarana zakazo kasanshi da kyau. Zaka ma iya koyan gudanar dashi.”
Thor ya kama kafadarsa; zafin yayi tsanani. Ya kalli kasa ya hangi hanunsa a rufe da jinni. Yaji kansa ba nauyi, yana damuwan abunda zai iya faruwa idan bai samu taimako ba.
Argon yayi taku uku zuwa gaba, ya mika hanu, ya riko hanun Thor da baya komai, ya daura shi da kyau a kan mikin. Ya rikeshi a wurin, ya mayar da kansa baya, sai ya rufe idannunsa.
Thor yaji wani yanayi mai dumi a cikin hannun nasa. Cikin dakikoki, jinin dake kan hannunsa ya bushe, kuma yaji zafin dayakeji ya fara raguwa.
Ya kalli hannun ya gagara ganewa: ya warke. Abinda ya rage a wurin kawai shine tabon idanun inda farcen dabban ya yankeshi – amma suma a toshe suke kuma sun yi Kaman sun kwana biyu. Jinin ma ya saya ya daina zuba.
Ya kalli Argon da mamaki.
“Yaya kayi wannan?” ya tambaya.
Argon yayi murmushi.
“Baninayiba. Kaikayi. Nina baiwa karfinka ummurni ne kawai.”
“Amma bani da karfin warkaswa,” Thor ya ansa, yana mamaki.
“Bakadashi?” Argon ya ansa masa.
“Bangane ba. Babu wani abu da yayi daidai da tunani a nan,” Thor yace, rashin hakurinsa na karuwa. “Yi hakuri, gaya mani.”
Argon yaki ya kalleshi.
“Wassu abubuwa a cikin lokaci zakazo kasani.”
Thor yayi tunanin wani abu.
“Yanzu wannan na nufin zan iya shiga rundunan sarki kenan?” ya tambaya, da faraha. “Tabbattace, idon zan iya kasha dabban Sybold, to zan iya kare kaina a wurin shauran yaran.”
“Tabbatace zaka iya,” ya ansa masa.
“Amma sun zabi yan’uwana – basu zabeniba.”
“Yan’uwanka bazasu iya kashe wannan mummunan dabban ba.”
Thor nata maida kallo, yana tunani.
“Amma ai sun riga sun kini. Dayaya zan shiga?”
“Daga yaushe jarumi ya fara bukatan a gaiyaceshi?” Argon ya tambaya.
“Kalmominsa sun shiga da zurfi. Thor yaji jikinsa gabadaya ya fara dumi.
“Kana nufin inje a ganni kawai kenan? Ba tareda an gaiyace ni ba?”
Argon yayi murmushi.
“Kai kana iya halittan kaddararka. Wasu basu iyawa.”
Thor ya kifta ido – kuma jimkadan, Argon ya bace. Kuma.
Thor ya juya, yana kallon kota ina, amma babu wani alamansa.
“A tanan!” inji wani murya.
Thor yajuya sai yaga wata katuwar dutse a gabansa. Yaji Kaman muryan yazo daga saman dutsen, sai yayi hanzari ya haura babban dutsen.
Ya kai saman, amma ya kidime da baiga ko alaman Argon ba.
Daga wannan wuri mai kyau, amma, ya iya gani samada itatuwan dajin Darkwood. Ya hangi inda Darkwood takare, yaga wata rana tana sauka a cikin launin ganye mai zurfi, kuma a gabada wannan kadan, hanyar zuwa fadan sarki.
“Kana iya bin hanyan,” muryan ya dawo. “Idan kanada zuciya.
Thor ya juyo amma baiga komai ba. Kaman murya ne kawai, yana dawowa. Amma yasan Argon na nan, a waniwuri, yana zigashi. Kuma yaji, daga zurfin zuciyarsa, cewa yanada gaskiya.
Batare da wani kwokwanto ba kuma, Thor ya sauko daga saman dutsen sai ya pasa cikin dajin ya nufi hanya mai nisan.
Yana gudu a hankali zuwaga kaddararsa.