Kitabı oku: «Wani Neman Jarumai », sayfa 4
SURA NA HUDU
Thor ya buya a cikin ciyawan bayan amalanken a yayinda yake gungurawa dashi akan babban hanya. Ya nemi hanya zuwa kan hanyan a daren jiya ya kuma jira da hakuri har amalaken dake da girmanda zai hau batare da anganoshiba ta zo. Wuri nada duhu a lokacin, kuma amalanken na tafiya a hankali dede da yadda zai iya dan gudu ya dale daga baya. Ya sauka cikin ciyayin ya kuma binne kansa a ciki. Yakuma ci sa’a, matukin bai gansaba. Thor bai sani a tabbaceba ko amalanken zata je fadan sarki bane, amma ta wurin yanufa, kuma amalanke mai wannan girman, da kuma irin wadannan alamun jikinta, zai kasance wurarenda zata iya zuwa bayawa.
Yayinda Thor ke safara cikin dare, idanunsa na bude na sa’o’i, yana tunanin karonsu da dabbar Sybold. Da Argon. A kan kaddararsa. Gidansu na daa. Mahaifiyarsa. Ya ji Kaman duniyan ta amsa masa, ta gaya masa cewa yanada wata kaddarar. Yanadai kwance a wurin, da hannayensa a bayan keyansa, yana kallon sama a dare, wanda ka ganuwa ta tsohon rufin amalanken. Ya kalli duniyan saman, yana kyalli, jajayen taurarinsa a can da nisa. Yana cikin annashuwa. A karo nafarko a rayuwarsa, yana kan tafiya. Bai san zuwa ina ba, amma yana tafiya. Kota wani hanya, zai nemi hanyan zuwa fadar sarki.
A yayinda Thor ya bude ido gari yariga yaw aye, haske na shiga, sai ya gano ashe barci ta kwasheshi. Ya tashi zuwaga zama da sauri, ya kalli kota ina, yayi wa kansa fada domin yayi barci. Yakamata a ce yafi haka kula – yaci sa’a ba a ganoshi ba.
Amalanken yacigaba da tafiya, amma girgizansa ya ragu. Wannan na nufin abu daya ne kawai: hanya dayafi kyau. Dole sunyi kusa da wata birni kenan. Thor ya leka yaga irin sumul din hanyan, babu duwatsu, babu ramuka, kuma a jere da fararen kauraa masu kyau. Zuciyarsa ta fara bugawa da sauri; sun fara kusa da fadan sarkin.
Thor ya leka waje daga bayan amalanken sai mamaki ya kamashi. Sabtatattun angwanin na cike da kaiwa da kawowa. Amalanku da yawa, masu girma da yanayi dabam dabam duk a dauke da ireiren abubuwa, sun cika kan hanyoyin. Daya a cike take da barguna; wata da shimfidun kasa; wata har wa yau da kaji. A tsakaninsu daruruwan yan kasuwa ke tafiya, wassu suna jagoran shanu, wassu suna da kwadunan kaya a kansu. Mutane hudu sun dauki kunshin yadin siliki, a nade a jikin gorori. Ya kasance runduna na mutane iri iri, duka kuma wuri daya suka nufa.
Thor yajikanshi Kaman ya samu wani sabon rai. Bai taba ganin mutane da yawa haka a lokaci guda ba, da kuma kaya da yawa haka, abubuwa dayawa suna faruwa a lokaci daya. Da kasance a karamin kauye duk rayuwarsa, amma yanzu ya kasance a cikin hayaniya na birni.
Ya ji babban kara, karan sarkoki, faduwan babban itace, da karfin da ya girgiza kasa. Jim kadan wani irin karan kuma yazo, na kwofaton dawakai masu kara a kan itace. Ya kallesu a kasa sai ya gane suna sallaka gada ne; a karkasinsu ruwan karamin rafin kariya na gudu. Da gadan da a ke nadawa.
Thor ya fitar da kansa yaga manyan shingayen dutse, babban mashiga na karfe mai kusosi kuma a sama. Suna wucewa ta kofar fadar sarki ne.
Wannan ya kasance kofa mafi girma da yataba gani. Ya kalli kusosin a sama, yana mamakin idan sun sauko, zasu rabashi biyune. Ya hangi yan Silver guda hudu suna gadin mashigin, sai zuciyarsa ta fara bugawa da sauri kuma.
Sun wuce ta cikin wata doguwar loton dutse, sai bayan wani dan lokaci kadan sama ya budu kuma. Suna cikin fadan sarki ne.
Thor ya gagara yarda. Akwai Karin kaiwa da komowa ma anan, mai yiyuwa – adadi mai kama da dubban mutane, suna zirga zirga ko ta ina. Akwai dogayen lambunan ciyayi, kansu ayanke daidai, da fure suna girma kota ina. Hanyan ya kara fadi, kuma daga gefegefen akwai kananan kantuna, masu saya da sayarwa da gineginen dutse. Kuma a cikin duk wannan, mayakan sarki. Mayaka, sanye da kayan yaki. Thor yaci nasara.
A cikin murnarsa, yatashi da ganganci; yanatashi, sai amalanken tasaya cak, shi kuma ya fado da baya, ya sauko a kan bayansa a cikin ciyayin. Kafin yatashi, sai yaji karan sauke kofan itace, sai ya daga ido yaga wani dattijo da yariga yaji haushi, mai tsanko, yana sanye da tsummokara kuma yana dadaura fuska. Matukin amalanken ya mika hanu ciki, ya kamo Thor a idanun sahu da hannaye ramammu, sai yaja shi waje.
Thor yadagu sama, ya sauko da karfi akan bayansa bisa kan hanya mai datti, ya kuma ta da kura. Sai dariyan mutane yatashi a kewaye dashi.
“Nan gaba in ka hau amalanke na, yaro, zaka shiga turune! Ka ci sa’a da na kira yan Silver a yanzun!”
Dattijon ya juya ya tofa yawu, sanan ya koma amalankensa ya bugi dawanken amalanken suka fara tafiya.
Dajin kunya, Thor ya tara mutucinsa ya taso zuwa kafafuwansa. Ya kalli guri. Mutum daya ko biyu masu wucewa sukayi masa karamin dariya, Thor yayi wani iri da fuskarsa har su suka mayar da nasu wassu wuraren. Ya karkade dattin jikinsa ya kuma share hanayensa; mutuncinsa ya tabu, amma ba jikinsa ba.
Annashuwansa ya dawo yayinda ya keta kallon wuri, yanata mamaki, sai ya gano yakamata yayi murnan cewa akalla shi ya kai nan. Yanzu daya riga ya sauka daga amalanken zai iya kallon wurare a saukake, kuma kallon ya kasance basabamba: akewaye yake da dogayen, ginanun katangun dutse masu gajerun katangun kariya a samansu, wanda kuma a samansu duka, kota ina, mayakan sarki keta sintiri. Gabadaya a kewaye dashi akwai filayen ciyayi masu launin ganye, masu samun matukar kulawa, shagunan da aka gina da duwatsu, mabulbulai na ruwa, gungu gungun bishiyoyi. Nan birni ne. Kuma a cike yake da mutane.
Kota ina shigowa ire iren mutane suketayi – yan kasuwa, mayaka, manyan mutane – kowa yakuma kasance yana sauri. Ya dauki Thor wasu yan mintuna kafin yagane cewa wani abu na mussamman na faruwa. A yayinda ya cigaba da tattakawa, yaga anata shirye shirye – ana jera kujeru, ana shirya mumbari. Yayi kama da ana shirin aure ne.
Bugun zuciyarsa yaso ya saya a yayinda yaga, daga dan nesa, wata filin gasa, da yar doguwar hanyanta mai datti da igiyan jan daga. A kan wani filin, yaga mayaka sunata wurga mashi ga ma’aunoni da nisa; a wani kuma, masu kwari da baka suna auna ciyayi. Yayi kama da wasanni ne kota ina, amma na gasa. Akwai kuma wakoki: algaita da busa da ganguna, tari tarin mawaka suna kaiwa da kawowa; da barasa, manyan tuluna da ake gungurowa waje; da abinci, tebura da ake shiryawa, liyafa a jere har iya ganin ido. Kaman ya shigo ne a sakiyar wani gagarimin biki. Duk da wannan kayatarwan, Thor yaji matsuwa na ya nemi inda runduna take. Yanajin Kaman ya makara, kuma ya kamata ya nuna kansa.
ya hanzarta zuwaga mutum na farko day a gani, wani dattijo wanda yayi kama, daga kayansa mai jinni, da mahauci, wanda ke gangarawa hanyan agaggauce. Kowa a nan na cikin hanzari ne.
“Ji mana, yallabai,” Thor yace, yakamo hanunsa.
Mutumin yayi kallo kasa zuwaga hanun Thor da kiyayya.
“Menene, yaro?”
“Ina neman rundunan sarki. Kasan inda suke horo?”
“Nayi kama da hatimin gane hanya ne?” mutumin yayi tsaki, yatafi yana buga kafa a kasa.
Thor yaji wani iri da rashin hankalinsa.
Ya hanzarta zuwaga mutum mabiye dashi da yagani, wata mata mai markada filawa a kan wani dogon tebiri. Akwai mata dayawa a tebirin, dukufe da aiki, sai Thor yaji yakamata ace daya daga cikinsu ta sani.
“Ji mana, yan mata,” yace. “Ko kinsan inda yan rundunan sarki ke horo?”
Sun kalli juna suka yi dan dariya, wasuma a cikinsu da shekaru kadan suka girmeshi. Babban cikinsu ta juya ta kalleshi.
“Kana nema a inda baiyi daidai ba” ta bada amsa. “Anan muna shiryawa bukukuwan ne.”
“Amma ance mani suna horo a fadan sarki ne,” Thor yace, a rikice.
Matan sun sake fara dan karamin dariya. Babban ta daura hannayenta a kugunta ta girgiza kai.
“Kanayi Kaman wannan ne karonka na farko a cikin fadan sarki. Baka da masaniyan girman da yake dashi ne?”
Thor ya rikice yayinda shauran matan suka fara dariya, sai ya fara tafiya da haushi. Bai cika son ana masa tsiya ba.
A gabansa yaga hanyoyi Kaman goma sha biyu, amummurde kuma ajujjuye zuwa kota ina a fadan sarkin. Ararrabe a sakanin katangun duwatsun akwai akalla kofofi goma sha biyu. Girma da yanayin wannan wurin nada ban al’ajabi. Yana jin damuwan shi zai iyata nema na kwanaki bai samu ba.
Wani tunani yazo masa: tabattace mayaki zai san inda shauran ke horo. Yana kasa a gwiwa akan zuwaga ainihin mayakin sarki, amma ya gane dole ne yaje.
Ya juya ya hanzarta zuwa bangon, zuwaga mayakin dake tsaron mashigi mafi kusa, yana fatan cewa kar ya wurgashi waje. Mayakin ya staya a mike, yana kallon gabansa sambai.
“Ina neman rundunan sarki,” Thro yace, a tarin dukannin muryar hazakarsa.
Mayakin ya cigaba da kallon gabansa sambai, Kaman bai jishiba.
“Nace ina neman rundunan sarki!” Thor ya nace, da Karin sauti, da nufin lallai sai an san dashi.
Bayan yan dakikoki, mayakin ya kalleshi kasa kasa, kallon raini.
“Zaka iya gayamin inda yake?” Thor ya masa.
“Kuma menene damuwanka dasu?”
Wani muhimmin batu,” Thor ya mayar, da fata mayakin ba zai matsa masa ba.
Mayakin ya koma kallon gabansa sambai, yaki kulashi kuma. Thor yaji gabansa na faduwa, yana soron ba zai samu amsa ba.
Amma bayan lokaci mai kama da har abadan, mayakin ya mayar cewa: “Ka bi mashigi na gabas, sai ka mike arewa iya iyawanka. Sai ka shiga mashigi na uku a gefen hagu, sanan inda hanya ya rabu ka bi dama, a wani rabuwan kuma kabi dama. Ka shige ta lankwashashen saman mashigi na dutse, sai kaga wurin horonsu a gaba da mashigin. Amma ina mai gayamaka, kana bata lokacinka. Basu yin maraba da maziyarci.
Abinda Thor ya bukaci ji kenan kawai. Batareda jiran wani bugun zuciyarsa ba kuma, ya juya ya wuce filin a guje, yana bin kwatancen, yana maimaitasu a cikin kwakwalwarsa, yana kokarin tuna su. Ya ga rana ya haura sosai a sama, sai yafara adu’an kawai lokacida shi zai kai, kar ya zama ya makara.
*
Thor ya gangara tsabtatattun, hanyoyi da jeren kaura a dan guje, yana murduwa da juyawa a kan hanyansa na tafiya a cikin fadan sarki. Yayi iya kokarinsa na ganin yabi kwatancen, yana fatan ba batar dashi a ke yi ba. Daga can karshen harabar, yaga dukkanin mashigun, sai ya zabi na uku a gefen hagu. Ya shigeshi a guje sai yabi wurarenda hanyan ya rabu kamar yada a ka gaya masa, yana juyawa hanya bayan hanya. Yayi gudu yana fuskantan masu zuwa, dubban mutane masu kwararowa cikin birnin, taron nata karuwa a kowane minti. Ya goga kafadu da masu hura algaita, masu carafke, masu shaila da ire iren masu nishadantar da mutane, kowanne ya ci ado na musamman.
Thor ya gagara hakuri da tunanin a fara zabe batare dashiba, sai yanata kokarin ya tara hankalinsa a yayinda yake juyawa hanya bayan hanya, yana neman wani alama na filin horon. Ya wuce a karkashin wani lankwashashen saman mashigi, ya juya wata hanyar, sai ga, can da nisa, ya hangi abinda kawai zai iya zama inda ya nufa ne: dan karamin haraba, a gine da duwatsu a kewaye dai dai. Mayaka na tsaron katon mashigi dake sakiyarsa. Thor yaji dan ihu daga bayan katangunsa sai bugun zuciyarsa ya karu. Nan ne wurin.
Ya fita a guje, huhunsa a bude. Yayinda yakai mashigin, mayaka biyu sun matso gaba suka sauke su mashinsu, suka tare hanya dasu. Wani mayaki na uku ya maso gaba ya daga hanu daya.
“Saya a wurin,” ya bada umrni.
Thor ya daskare, yana numfashi sama sama, Kaman zai gagara boye murnarsa.
“Ba…zaka…ganeba,” ya sauke numfashi, kalmomi na fadowa daga bakinsa a sakanin numfashi, “Dole na kasance a ciki. Na makara.”
“Makara ma me?”
“Zaben.”
Mayakin, wani gajeren, mutum mai nauyi da zazzana a fata, ya juya ya kalli shauran, suma suna mayar da kallon rashin yarda. Ya juya ya kalli Thor daga sama zuwa kasa da wani kallon rashin yarda shima.
“An shigar da sabobin daukan tun sa’o’in da suka wuce, a safaran sarauta. Idan ba a gayyace ka ba, ba za ka shiga ba.”
“Amma ba ka ganeba. Dole ne na---”
Mayakin ya mika hanu ya kama gaban rigan Thor.
Kaine baka geneba, kai yaro mara kunya. Kai waye da zaka zo nan ka nemi shiga ko ta halin kaka? Yanzu katafi----kafin na saka a turu.
Ya ture Thor, wanda ya fada baya da taku dayawa.
Thor yaji Kaman harbi a cikin kirjinsa a inda hanun mayakin ya tabashi--- amma fiye da haka, yaji harbin an kishi. Yaji wannan rashin adalci ne. Bai iso har nan kawai domin wani mayaki yazo ya mayar dashi batare da ma anganshi bane. Ya daura zuciyan saishi ya shiga.
Mayakin ya juya zuwaga mutanensa, shi kuma Thor ya tafi, ya juya dama ya kewaya kewayayen ginin. Yana da wata shiri. Ya cigaba da tafiya har ya bace, sai ya fara dan gudu, yana bin jikin dangan. Ya duba domin ya tabbattar mayakan basu kallonsa, sai ya kara gudu sosai, daya kai rabin hanyan kewayan ginin ya hangi wata mashigin haraban---a can sama akwai lankwasassun budi a dutsen, a kare da sadunan karfe. Daya daga cikin wadannan budin ya rasa karafunansa. Yaji wani ihun, ya haura zuwaga dan belen, yayi kallo.
Bugun zuciyarsa ya karu. Ararrabe a cikin babban, kewayayyen wurin horon yaga dozin dozin na sabobbin dauka----har da yan’uwansa. Sun yi sahu, duk sun fuskanci yan Silver guda goma sha biyu. Mayakan sarkin suna tafiya a cikinsu, suna auna su da idanu.
Wata kungiyan sabobbin daukan kuma na saye daga gefe, karkashin kulawan wani mayaki, suna wurga mashoshi ga wani abun aunawa da nisa. Waninsu bai samu ma’aunin ba.
Hanyoyin jinin Thor sun kumbura da haushi. Shi zai iya harbin wadannan abin aunawan; shi gwanine Kaman kowanne daga cikinsu. Kawai domin sun girmeshi, kuma shi ya dan fisu kankanta, ba a yi adalci ba da a ka barshi a ka ki daukansa.
Basanmani, Thor yaji wata hanu a bayansa a yayinda hanun ta finciko shi zuwa ta baya ta kuma aika dashi a cikin iska. Ya fado da karfi a kasa, tare da rasa numfashi.
Ya kalli sama yaga mayakin bakin mashigin dazun, yana harararsa.
“Me na gaya maka, yaro?”
Kafin ya mayar da martini, mayakin yaja da baya ya harbi Thor da kafa kuma da karfi. Thor yaji wani hadadden kara a hakarkarinsa, a yayinda mayakin ke shirin sake bugashi.
Wannan lokacin, Thor ya kamo kafan mayakin a iska; ya finciko kafan, ya bata sayuwanshi sai yasa ya fado.
Thor ya taso zuwa kan kafafuwansa da sauri. A lokaci daya kuma, mayakin ma yatashi. Thor ya kalleshi, yana tsoron abinda shi ya aikata yanzu yanzu. A daya bangarensa, mayakin na huci da haushi.
“Ba kawai zan saka a turu ne kadai ba,” mayakin yace da rufafen baki, “har ma zan saka ka biya abinda kayi. Bawanda ya isa ya taba maitsaron fadan sarki! Ka manta da shiga runduna---yanzu zaka ruba a kurkuku! Zai zama babban sa’a in har an sake ganinka!”
Mayakin ya ciro wata sarka mai turu a karshen. Ya nufi Thor, da ramuko a nune a fuskarsa.
TunaninThor ya fara gudu. Ba zai iya yadda a sa shi a turu ba---duk da haka baya son ya jiwa wani daga cikin masu tsaron sarki. Dole yayi tunanin wani abu---kuma da gaggawa.
Sai ya tuna majajjabarsa. Hazakansa ya rigayeshi a yayin da ya kamoshi, yasa dutse, ya auna, sai ya sake dutsen.
Dutsen ya tafi a iska sai ya bige turun daga hanun mayakin dake cikin mamaki har yanzu; ya kuma samu yasun mayakin. Mayakin ya ja da baya yana girgiza hanunsa, yana ihu saboda zafi, a yayin da turun suka zuba a kasa.
Mayakin, tare da yiwa Thor kallo irin na mutuwa, ya fitar da takwafinsa. Takwafin yafito da ainihin, karan karfe.
“Wancan ya kasance kuskurenka na karshe,” yayi mumunan barazana, sai ya taso.
Thor bashi da wani zabi; wannan mutumin yaki ya barshi. Yasa wata dutsen a majajjabarsa ya wurga. Yayi awu da gangan---baya son ya kashe mayakin, amma dole ya sayar dashi. Saboda haka maimakon ya auni zuciyarsa, ko hanci, ko ido, ko kai, Thor ya auna wuri daya da yasan zai sayar dashi, amma ba zai kasheshi ba.
Tsakanin kafafuwan mayakin.
Ya saki dutsen ya bi iska---ba da dukkanin karfinsa ba, amma daidai abinda zai ka da mutumin.
Harbin ya kasance yaje dai dai.
Mayakin ya fado, yana mai sake takwafinsa, a yayinda ya kama kwalatansa ya fadi a kasa ya dunkulu Kaman kwallo.
“Zaka ratayu saboda wannan!” ya fadi acikin zafin ciwo. “Mayaka! Mayaka!”
Thor ya daga kai yaga daga dan nesa dayawan masu tsaron gidan sarki sun nufe shi.
A yanzu ne kokuma har abada.
Ba tare da bata wani lokaci ba kuma, ya ruga a guje zuwa bakin taga. Dole ya sallaka ta cikin tagan, zuwa cikin haraban, ya nuna kansa. Kuma zai yaki duk wani wanda ya tare masa hanya.
SURA NA BIYAR
MacGil na zaune a zauren sama na gidan sarautansa, a zauren taro da ‘yan kusa dashi, wanda yake amfani dashi wurin lammuran kansa. Ya zauna a kujeran sarauta da yake so sosai, wannan an kera shi daga itace, yana kallon yaranshi hudu da suke tsaye a gabansa. Akwai babban dansa, Kendrick, mai shekaru ashirin da biyar jan gwarzo kuma kamilin mutum. Shi, a cikin duk yaransa, yafi kama da MacGil---wanda ya kasance abin mamaki, tuda dan cikin shege ne, da daya tilo da MacGil ya aifa da wata mata a waje, matarda ya dade da mantawa da ita. MacGil ya raini Kendrick da asalin yan halak dinsa, duk da kokekoken sarauniya daga farkon lamarin, akan alkawarin ba zai taba hawa sarautan ba. Wannan naci wa MacGil tuwo a kwarya yanzu, tunda Kendrick ya kasance namiji mai kyau na farko da yasani, yaron da yake alfaharin shi ne ya haifeshi. Da ba wani yariman da zai fishi cancantuwa da mulkin masarautar.
Banda shi, sabanin wannan, haifafen dansa na biyu ya saya—amma dan halak dinsa na fari—Gareth, shekaru ashirin da uku, siriri, da fadadun kumatu da manyan idanu masu launin kasa da basu taba daina motsi. Halinsa ba zai iya banbanta da na yayansa fiye da haka ba. Yanayin Gareth ya kasance duk abinda na Kendrick bai kasance ba: a yayinda yayansa ke fito wa fili, Gareth na da boye tunaninsa na asali; a yayin da yayansa keji dakansa da kuma kama kai, Gareth nada rashin gaskiya da yaudara. Yakan daga wa MacGil hankali yaki dansa, kuma yayita kokari sau barketai ya gyara yanayinsa; amma bayan wani matsayi a shekarun kuruciyan yaron, ya hakura da cewa haka kaddaran yaron yake: kulle kulle, kwadayin mulki da buri ta hanyoyin da suka saba. Gareth kuma, MacGil ya sani, baya sha’awan mata, kuma yanada masoya maza dayawa. Wasu sarakunan da sun kore irin wannan dan, amma MacGil yafi ganewa, kuma a wurinsa, wannan bai kai dalilin da zai sa shi ya ki dansa ba. Baya masa hukunci a kan wannan. Abinda yake masa hukunci akai shine yanayin mugunta, da kulle kullen da yake dashi, wanda ya kasance abinda ba zai iya juya wa baya ba.
A jere a gefen Gareth akwai haifefiyar diyar MacGil na biyu, Gwendolyn. Wanda kwananan ta kai shekaru goma sha shida, ta kasance da kyaun da yayi daidai da duk wani wanda ya taba gani da idanunsa—kuma yanayinta yafi suranta haskakawa. Tanada kirki, bude hanu, gaskiya---budurwa mafi kyau da ya taba sani. Ta wannan hanyan, daya take da Kendrick. Ta kalli MacGil da soyayyar diya zuwaga mahaifinta, kuma yakan ji goyon bayanta gareshi a kowane kallo da ta masa. Ya mafi alfahari da ita a kan yaransa maza.
A saye a gefen Gwendolyn akwai dan autan MacGil namiji, Reece, matashin yaro mai ji da kansa kuma mai annashuwa, a shekaru goma sha hudu, ya fara zama namiji. MacGil ya kalla da farin ciki shigarsa runduna, kuma har ya fara hangan irin mutumin da zai juya ya zama. Wata rana, MacGil bashi da kwokwanto, Reece zai zama dansa mafi kyau, kuma babban shugaba. Amma wannan ranan ba yanzu bane. Shi yaro ne a yanzu, kuma yana bukatan sanin abubuwa dayawa.
MacGil na jin yanayi kalakala a yayin kallon yaransa duka hudu, yaransa maza uku da namace daya, a saye a gabansa. Yana jin alfahari a gauraye da bankasawa. Ya kuma ji fushi da haushi, saboda yaransa biyu basu kasance a nan ba. Babban cikinsu, diyarsa Luanda, tabattace na shirya wa aurenta, kuma tunda auren zai kaita wata masarautane, bata da wani alaka da wannan tattaunawan magada. Amma daya dansa, Godfrey, a shekaru goma sha takwas na sakiyan, bayanan. MacGil yaji haushin rashin amsa kiran.
Tun yana yaro, Godfrey ke nuna wa sarauta rashin daraja; a tabbace yake cewa bai damu da sarautaba kuma ba zai taba hawa mulki ba. Kuma, babban rashin jindadin MacGil, ya kasance zabi Godfrey na yin wasa da ranakun rayuwarsa a gidajen barasa da abokanai marasa nisuwa, wanda yake jawo wa gidan sarautan Karin jin kunya da rashin mutunci. Yakasance ragwo, yana barci a mafi yawan sakar ranaku ya kuma cikita shaurar ranan da shan barasa. A daya bangaren, MacGil ya dan sake saboda rashin kasancewarsa; a dayan kuma, cin fuska da ba zai yadda dashiba. Ya kasance, dama, yana sa ran hakan na iya faruwa, sai ya aiki mayakan sa su tace gidajen barasa su kawoshi. MacGil ya zauna shuru, yana jira, sai sun kawoshi.
Dagakarshe babban kofar oak din ta budu sai ga masu tsaron fadan suna takowa ciki, sunsa Godfrey a sakaninsu. Sun hankadoshi, sai Godfrey yayi tangal tangal zuwa cikin dakin ayayinda suka rufe kofan a bayansa.
Kannensa maza da namace sun juyo suna kallo da buddadun idanu. Godfrey acikin halin ko’oho, na warin barasa, ba gyaran fuska kuma rabi a tube. Ya mayar da murmushi. Da rasin hankali. Kaman yadda aka saba.
“Barka, Baba,” Godfrey yace. “Nishadin ya wucenine?”
“Zaka saya da yan’uwanka ka jira sai nayi Magana. In kaki, Allah ya taimakeka, zan daureka da sarka a cikin kurkuku da shauran talakawan yan kurkuku, kuma ba zaka ga abinciba---balle barasa---na kwana uku gabadaya.”
Darashinji, Godfrey ya mayar da kallo ido abude sosai ga mahaifinsa. A wannan kallon, MacGil ya gano wani ma’ajiyin, wani gado daga gareshi, hasken wani abu da watakila wata rana zaiyiwa Godfrey anfani sosai. Hakan zai zama, in har ya iya barin wannan yanayinsan.
Dan tawaye nakinkari, Godfrey ya jira na dakikoki goma masu kyau kafin yabi umurni yayi tafiyan ganin dama zuwa ga shauran.
MacGil yayiwa yara biyar dake gabansa kallo mai kyau: dan cikin shegen, mai dabam da kowan, mashayin, diyarsa da kuma dan autansa. Hadin da baiyi daidai bane, yarda cewa duk sun fito daga jikinsane yaso yamasa wuya. Kuma a yanzu, a ranan auren babbar diyarsa, alhakin ya fado kansa ya zabi yarima daga wanan tarin. Tayaya hakan zai yiwu?
Wannan yakasance aikin banzane; bayan ma, shima yana kuruciyansane kuma zai iya mulki har shekaru talatin nan gaba. In ta dauro duk yariman da ya zaba ba zai hau sarautanba nan da shekaru dayawa. Al’adan ma gabadaya bai masa ba. Watakila tayi amfani a zamanin mahaifansa, amma batada mazauni a yanzu.
Ya gyara murya.
“Mun taru anan yau saboda wata bukatan al’ada. Kaman yadda kuka sani, a yau, a ranan auren babbar diya, hakkin ya fada akaina na zabi magaji. Yariman da zai gaji mukin masarautan nan. Inda zan mutu, babu wanda yafi cancanta yayi mulki Kaman mahaifiyarku. Amma dokokin masarautarmu sun tanadi cewa sai haifafen dan sarki ne zai iya cin gadon sarauta. Sabodahaka, dole na zaba.”
MacGil ya riki numfashinsa, yana tunani. Wani shuru ya mamaye wurin, kuma yanajin inda wurin ya cika da nauyin zalama. Ya kalli cikin idanuwansu, yaga yanayi dabamdabam a kowanne. Dancikin shegen ya rungumi kaddara, saboda yasan ba za a zabeshiba. Idanun mai dabam da kowa sun cika da buri, Kaman yana jiran zaben ya fada kansa saboda haka ya kamata. Mashayin na kallon waje ta taga, bai damuba. Diyarsa na mayar da kallo cike da soyyaya, da sanin cewa ita ba wani bangaren wannan tattaunawan bane, amma duk da haka take son mahaifinta. Hakama dan autansa.
“Kendrick, nakan daukeka a matsayin assalin da tunda. Amma dokokin masarautanmu sun hanani mika wa duk wanda asalinsa yadan kasa sarautan nan.”
Kendrick kai a sunkuye yace. “Baba, bansaran zaka yi hakaba. Na gamsu da abinda Allah yamani. Narokeka kar wannan ya daga maka hankali.”
Hankali MacGil ya tashi da amsarsa, yaji cewa zuciyarsa ya fada da gaskiya kuma wannan yasashi jin Karin Kaman ya nadashi a yariman.
Shauran ku hudu kenan. Reece, kai matashine mai kyau, mafi kyawun da na taba gani. Amma girmanka yadan kasa wa wannan tattaunawan.”
“Haka nima nake tunani, Baba,” Reece ya mayar, da karamin sunkuyar da kai.
“Godfrey, kai dayane daga cikin asalin yara na maza uku---duk da haka kazabi kasha ranakunka a gidan barasa, da najasa. Kasamu duk wani zarafi na rayuwa, kuma ka barnatar da duka. Idan inada wata danasani a rayuwana, to kai ne.”
Godfrey ya mayar da kallo da gwayewan ido, yagagara nitsuwa wuri daya.
“To, dai, ina ganin nagama a nan, zan koma gidan barasa, ko bahakaba, Baba?”
Da sunkuyar kai da sauri, na raini, Godfrey ya juya ya fara fita a dakin.
“Ka dawo nan!” MacGil yayi ihu. “YANZU!”
Godfrey yacigaba da tafiya, Kaman bai jishiba. Ya sallaka dakin yaja kofan ya bude. Masu tsaro biyu suna saye a kofan.
MacGil ya kumbura da haushi a yayinda masu tsaron ke kallonsa da idanun tamabaya.
Amma Godfrey bai jiraba; ya bangari sakaninsu ya wuce, zuwa cikin budadiyar haraba.
“Ku tsareshi!” MacGil yafada da babban murya. “Kuma karku yarda sarauniya ta ga hakan. Bana son mahaifiyarsa da tunanin yadda taganshi a ranar auren diyarta.”
“To, maigida,” sukace, suka rufe kofar a yayinda suka hanzarta suka bishi.
MacGil ya zauna a wurin, yana numfashi, idanunsa jazur, yana kokarin ya kwantar da hankali. A karo na Kaman dubu yayi tunanin laifinda shi yayi aka sakamasa da irin wannan dan.
Ya dawo kallon shauran yaransa. Dukansu hudu sun mayar da kallo zuwa gareshi, suna jira acikin shuru mai nauyin. MacGil yaja numfashi mai zurfi, yana kokarin hada hankalinsa wuri daya.
“Shauran ku biyu kenan,” ya cigaba. “Kuma daga ku biyun, na riga na zabi magaji.”
MacGil ya juya zuwa ga diyarsa.
“Gwendolyn, zai kasance ke ne.”
Ko ina yayi sit a dakin; yaransa duk sun ji mamaki, musamman ma Gwendolyn.
“Kayi magana daidai kuwa, Baba?” Gareth ya tambaya. “Gwendolyn kace?”
“Baba, ka girmamani,” Gwendolyn tace. “Amma bazan karba ba. Ni namace ce.”
“Gaskiya, namace bata taba zama akan sarautan dangin MacGil ba. Amma na hada zuciya na akan lokaci yayi da za a canja al’ada. Gwendolyn, zucinyanki da ruhunki sun kasance mafi kyawunda na taba gani a jikin budurwan da na taba sani. Kina kuruciya, amma in Allah ya yarda, bazan mutu a yanzu ba, kuma kafin lokacin yazo, basirarki da hikimarki zasu kai na yin mulki. Masarautan zai zama naki.
“Amma Baba!” Gareth yayi ihu, fuskarsa a daure. “Nine danka na halak na farko! A ko dayaushe, a tarihin dangin MacGil gaba daya, sarauta zuwaga babban da yake zuwa!”
“Nine sarki,” MacGil ya amsa kwasam, “ni nake kirkiro al’ada.”
“Amma ba a yi adalci ba!” Gareth ya nemi ahuwa, muryarsa na girgiza. “Ni yakamata na zama sarki. Ba yar’uwana ba. Ba namace ba!”
“Yishuru da bakinka, yaro!” MacGil yayi ihu, yana girgiza da haushi. “Ka isa ka ja da hukunci na?”
“Ana hana ni saboda namace kenan? Haka tunaninka akaina yake?”
“Nariga na fadi ra’ayi na,” MacGil yace. “Zaka mutunta ra’ayin kuma kayi ladabi cikin binsa, Kaman kowa a cikin masarautana. Yanzu, duk kuna iya barin wurina.”
Yaransa sun dan sunkuyar da kawunansu da sauri suka fita a dakin agagauce.
Amma Gareth ya saya a kofa, ya gagara kawo kansa ga fita.
Ya juyo, sai, shi kadai, ya fuskanci mahaifinsa.
MacGil naganin rashin cikan buri a fuskarsa. A fili yake, ya sammani a kirashi magaji a yau. Harma: yana son hakan. Da zalama. Abinda bai bawa MacGil mamaki ba kokadan---wannan nema dalilin da yasa bai zabeshi ba.
“Mai yasa ka tsaneni, Baba?” ya tambaya.
“Ban tsaneka ba. Ina ganin baza ka iya mulkin masarautana bane kawai.”
“Kuma domin me kenan?” Gareth ya dada dannawa.
Saboda ainihin abida kake nema kenan.”
Fuskan Gareth ya juya baki. A zahiri, MacGil ya bashi labarin yanayinsa na ainihi. MacGil ya kulada idanunsa, yaga suna nuna kiyayyan da shi bai taba sammani ba masa.
Batare da wata kalma ba kuma, Gareth ya bar dakin yana buga kafafumwansa a kasa ya rufe kofa da karfi a bayansa.
A girgizan bayan hakan, MacGil ya girgiza. Ya sake tuna hararar dansa sai ya gane akwai kiyayya mai zurfi, wanda yafi na abokan gabansa ma zurfi. A wannan lokacin, yayi tunanin Argon, yayi tunanin maganansa daya fada, na kusancin hatsari.
Kusanci zai iya zama Kaman haka ne?