Kitabı oku: «Wani Neman Jarumai », sayfa 5

Yazı tipi:

SURA NA SHIDA

Thor ya wuce fadin haraban da gudu, yana gudu da dukan ikonsa. A bayansa yana jin takun masu tsaron fadan sarki, a kurkusa dashi. Sun bishi duk fadin fili mai zafi da kuran, suna tsinuwa yayin binshi. A gabansa akwai ‘ya’yan runduna—da sabobin dauka—na rundunan mayaka, dozin dozin na yara maza, kamansa, amma sun fishi shekaru da girma. Suna kan horo kuma ana gwadasu a yanayi iri iri, wasu suna wurga mashi, wasu na wurga jabilin, kadan suna koyon kama mashin. Suna auna ma’aunai daga nesa, batare da rashin samun ma’aunain dayawa ba. Wadanan ne abokan gasansa, kuma sun yi kama da wadanda kayar dasu zai yi wuya.

A cikinsu akwai manyan mayaka, ‘ya’yan Silver, sun hada rabin zobe akewaye suna kalon karawa. Suna alkalanci. Suna yanka hukuncin waye za a zaba kuma waye zai koma gida.

Thor yasan dole ya nuna kansa, ya samu yabon wadanan mutanen. Cikin dan lokaci masu tsaron zasu kai gareshi, kuma idan zai samu zarafin nuna kansa, to a yanzu ne. Amma ta yaya? Zuciyarsa nata kaiwa da komowa ayayinda ya wuce sakiyar haraban a guje, yana da muradin lallai kar a kore shi.

A yayinda Thor ke gudu a filin, shauran sun fara kula. Wasu daga sabobin daukan sun daina abinda sukeyi suka juyo, kamar yada wasu mayan mayakan sukayi suma. Cikin dan lokaci, Thor yaji hankalin kowa a kansa. Yanayinsu ya nuna mamaki, sai yagane watakila suna mamakin ko shi wayene, yana fasa sakiyar haraban, masu tsaron guda uku suna binshi. Wannan bashine yanda yaso ya nuna kansa ba. Duk rayuwarsa, ya kasance yana mafarkin shiga runduna, amma bai taba fatan ya faru haka ba.

Ayayinda Thor ke gudu, yana tunanin abinyi, matakin da yakamata ya bayanu masa karara. Wani katon yaro, sabon dauka, ya dauki nauyin nuna kansa wa shauran ta dalilin sayar da Thor. Dogo, da jijiyoyi kota ina, ya kusan ribanya girman Thor sau biyu, ya daga takwafin itace domin ya tare wa Thor hanya. Thor yaga lallai yayi muradin kadashi, yayi masa tsiya a gaban kowa, yakuma samawa kansa yabo akan shauran sabobin daukan.

Wannan ya bawa Thro haushi. Thor bashi da damuwa da wannan yaron, kuma ba yakin yaron bane. Amma yaron ya maida yakin nasa, kawai domin samun yabo a kan shauran.

Daya maso kusa, girman yaron ya bawa Thor mutukar mamaki: yafishi sayi sosai, a rufe da bakin gashi mai kauri daya rufe goshinsa, da kuma mafi girman, habba da Thor ya taba gani. Bai ga hanyan da shi zai bi yayiwa yaron nan ko dan illa ba.

Yaron ya nufoshi da takwafin itacensa, kuma Thor yagane cewa idan shi baiyi wani abudu da sauri ba, za a sumar dashi.

Zafin naman Thor sai ya rigayeshi. Ya ciro majajjabarsa, ya kwanta baya, sai ya harbo dutse ga hanun yaron. Dutsen ya samu inda ya auna ya bige takwafin daga hanun yaron, daf da zai kawo hanu kasa ya bige Thor. Takwafin ya tafi a iska kuma yaron, yana ihu, ya rike hanunsa.

Thor bai bata wani lokaci ba. Ya taso, yana amfani da zarafin lokacin, yayi tsalle sama a iska, ya harbi yaron da kafa, ya binne duka kafafuwansa a mike a gabansa zuwaga kirjin yaron daidai. Amma kaurin yaron yasa, yayi Kaman harbin itacen gamji da kafa ne. Yaron ya koma da baya da wasu incina ne kawai, ayayinda shi kuma Thor ya gagara yin gaba sai ya durkusa a kafofin yaron.

Wannan ba alama mai kyau bane, Thor yayi tunani, yayinda yafado da wani kara, kunnuwansa na buga kararrawa.

Thor yayi kokarin tashi, amma yaron ya rigashi. Ya mika hanu kasa, ya riko Thor daga baya, yayi wurgi dashi, yatafi a iska, ya fado da fuska, a cikin dauda.

Gungun yara maza suka taru da sauri akewaye dasu Kaman zobe kuma suna ihu. Thor ya girigiza, yaji kunya.

Thor ya juya domin ya tashi, amma saurin yaron yayi yawa. Yariga ya kasance a samanshi, yana danneshi. Kafin Thor yasan wani abu, abin ya zama gasan kokuwa, kuma nauyin yaron na dayawa.

Thor najin ihun shauran sabobin daukan ayayinda suka kewayesu Kaman zobe, suna ihu, suna kwadayin a zub da jinni. Fuskan yaron ya nuna haushi da ya kalleshi a kasa; yaron ya miko manyan yatsunsa ya cusa a idanun Thor. Thor ya gagara yarda---kaman yaron na ainihin son yajimasa ciwo. Neman yabonsa har yakai na haka ne?

A dakika na karshe, Thor yakauda kansa, hannayen yaron suka wuce a iska, suka binnu a cikin dauda. Thor yayi amfani da zarafin ya gungure ya fita daga karkasin yaron.

Thor ya mike kan kafafuwansa ya fuskanci yaron, wanda shima ya tashi. Yaron ya taso yana neman fuskan Thor, sai Thor ya kauce a dakika na karshe; hucin naushin ya wuce a fuskarsa, sai yagane da naushin yaron yasameshi, da ya karyamasa dashashi. Thor ya mika hanu sama ya naushi yaron a makogoro, amma bai masa komai ba; Kaman nausan bishiya ne.

Kafin Thor yasake mayar da martini, yaron ya dokeshi a fuska da gwiwar hanu.

Thor ya koma da baya, yayi tangal tangal zuwa baya daga naushin. Naushin ya kammaci bugun guduma, kuma kunnuwansa sun fara karan kararawa.

Yayinda Thor ke tangal tangal, yana neman ya mayar da numfashi daidai, yaron ya taso ya doke shi a kirji da kafa. Thor yatafi da baya a iska ya zubo a kasa, ya sauka da baya. Shauran yaran suna tafe da ihu.

Thor, dajiri, ya fara tashi zuwa ga zama, amma yaron ya kuma tasowa, yajuya, yasake naushinsa, da karfi a fuska, yasake kadashi gabaya a kan bayansa---kuma akaye har Abadan.

Thor ya kwanta a wurin, yana jin ihun shauran yaran, yanajin dandanon gishiri na jinni daga jininda yake fito daga hancinsa, da zanenda yamasa a fuska. Yayi kuka saboda zafin ciwo. Ya dubi sama yaga katon yaron ya juya ya fara tafiya zuwaga abokanensa, yariga ya fara mrunan samun nasaransa.

Thor yaso ya hakura. Yaron nan katone, fada dashi aikin banza ne, kuma shima horon ta isa haka. Amma wani abu a cikin jikinsa nata ingizashi. Ba zai hakura da rashin nasara ba. Ba a gaban duka wadanan mutanen ba.

Kada ka hakura. Ka tashi. Ka tashi!

Thor ya taro karfi ya lallaba dai. Yana gurnani, ya juya ya hau kan kafafuwa da gwiwowinsa, sai, ahankali, ya saya kan kafafuwansa. Ya fuskanci yaron, jinni na zuba daga jikinsa, idanunsa a kumbure, baya gani da kyau, yana numfashi sama sama, sai ya dago kunshin dambensa.

Katon yaron ya juyo ya kalli Thor a kasa. Ya girgiza kai a dalilin mamaki.

“Da ka kwanta shuru, yaro,” yayi barazana, ayayinda ya fara zuwaga thor kuma.

“YA ISA!” wani murya yayi ihu. “Elden, ka kwance damara!”

Wani gwanin mayaki yayi zuwan bazata, ya shiga sakaninsu, ya mika hanu yana hana Eden masowa kusa da Thor. Taron mutanen sun yi shuru, ayayinda duk suke kallon gwanin mayakin; a bayyane yake cewa wanan mutum ne da ake baiwa biyayya.

Thor ya kalli sama, yana mamakin kasancewan gwanin yakin. Shekarunsa na ishrin da wani abu, mai sayi, da kafadu masu fadi, kewayayyen haba, da mai launin kasa, na daga mafi samun kulan gashi. Nan da nan Thor yaji shi yana sonsa. Kayan adon yakinsa mafi asali, kayan tsarka da akayi daga azurfa mai kyalli, na rufe da alamun gidan sarauta: alaman shurwa na dangin MacGil. Wuyan Thor ya bushe: yana saye a gaban dan gidan sarauta ne. Ya gagara yarda da haka.

“Kayi bayanin kanka, yaro,” yacewa Thor. “Yaya ka shigo mana cikin haraba ba gayyata?”

Kafin Thor ya mayar da wani martini, kwassam, masu tsaron fadan sarki ukun suka shigo zoben. Magabacin mai tsaron ya saya a wurin, yana numfashi samasama, yana nuna Thor da yasa.

“Yaki bin umrninmu!” mai tsaron yayi ihu. “Zan sashi a turu na kuma kaishi kurkukun sarki!”

“Banyi wani laifi ba!” Thor ya nuna rashin amincewa.

“Kokasani?” mai tsaron yayi ihu. “Shiga wani kadaran sarki ba tare da gayyata ba?”

“Abinda naso insamu kawai zarafine!” Thor ma yayi ihu, ya juya, yana rokon gwanin mayakin dake gabansa, dan dangin sarautan. “Abinda nasosamu kawai shine zarafin shiga runduna!”

“Wannan haraban horon na gayyatatu ne kawai, yaro,” inji wani murya mai fadi.

Wani gwarzo ya shigo cikin zoben, da shekaru hamsin da, mai fadi kuma dunkulalle, da tsanko a kansa, gajeren gemu, da tabon ciwo da ya wuce ta kan hancinsa. Yayi Kaman ya kasance gwanin mayaki duk rayuwansa---kuma daga alamun jikin kayansa, kusan gwal dake kirjinsa, Kaman shine babban mai bada ummurni. Bugun zuciyan Thor ya karu da yagansa: Babban janar.

“Ba a gayyaceni ba, maigida,” Thor yace. “Wannan gaskiyane. Amma mafarkina a gaba dayan rayuwana shine in kasance a nan. Ina bukatan zarafine kawai na nuna maka abinda zan iyayi. Ina da iyawa Kaman kowanne a cikin wadanan sabobin daukan. Kabani zarafi daya kawai domin na tabattar da hakan. Yi hakuri. Shiga runduna shine abu daya tilo da naketa mafarkinsa.

“Wannan filin dagan bana masu mafarki bane, yaro,” martaninsa na tsiya yazo. “Wuri ne na mafadata. Babu sasauci a dokokinmu: sabbin shiga zabensu akeyi.

Janar din yayi nuni da kai, sai mai tsaron fadan ya nufi Thro, a rike da turu.

Amma ba zato gwanin mayakin, dan dangin sarautan, ya maso gaba ya daga hanunsa, ya tare mai tsaron.

“Watakila, a wannan karon, za a iya rangwame,” yace.

Mai tsaron ya daga ido ya kalleshi da mamaki, azahirance yanason yayi Magana, amma ya zama dole yayi shuru saboda biyayya ga dan gidan sarauta.

“Ina son yanayin ruhinka, yaro,” gwanin mayakin ya cigaba. “Kafin mukoreka, zanso naga abinda zaka iyayi.”

“Amma Kendrick, munada dokokinmu---” janar din yace, azahiri bai ji dadi ba.

“Dangin sarauta ke yin dokokin,” Kendrick ya amsa da karfin murya, “kuma rundunan na biyayya ne ga dangin sarauta.”

“Muna biyayya ga mahaifinka, sarki---ba kai ba,” janar din yamusanta, yana kuma jayayya.

Akwai babban ja, wuri yayi kauri da rashin tabbas. Thor ya gagara yarda da abinda shi ya tayar.

“Nasan mahaifina, kuma nasan abinda zaiso. Zaiso ya baiwa wannan yaron wani gwaji. Kuma abinda zamuyi kenan.”

Janar din bayan lokaci na rashin tabbas kadan, abisani ya hakura.

Kendrick ya juyo zuwaga Thor, idanunsa a kulle akan nashi, da launin kasa kuma akure, idanun yarima, amma na jarumi kuma.

“Zan baka zarafi,” ya gayawa Thor.”Mugani idan zaka iya samun wancan shaidan awun.”

Yayi nuni zuwaga wani tarin cayayi can da nisa a filin, da dan karamin, jan digo a sakiyarsa. Su mashi dayawa a kafe a cikin ciyayin, amma ba ko daya a cikin jan digon.

“Idan zaka iyayin abinda ba wanda ya iyayi a cikin shauran yaran---idan zaka iya samun jan shaidan---to zaka iya shiga cikinmu.”

Gwanin mayakin ya koma gefe, kuma Thor najin idanunsa a kansa.

Ya hangi matattarin mashu ya kuma kallesu a nise. Suna da kyawun da bai taba ganiba, anyisu daga dunkulalen itacen gamji, an kuma samasu mafi kyawun fata. Zuciyarsa nata bugawa yayinda yayiwo gaba, yana share jinin hancinsa da bayan hanunsa, yana barin da bai taba yi a rayuwarsa ba. Tabbattace. Ana bashi aikinda kusan bazai taba yiyuwa bane. Amma dole ne yayi kokari.

Thor ya mika hanu ya zabi mashi, ba doguwa ba, kuma ba gajeruwa ba. Ya ji nauyinta a hanunsa—nada nauyi, da dan dama. Ba Kaman wayanda yake amfani dasu a gida ba. Amma yajishi daidai shima. Yaji cewa maiyiwuwa, maiyiwuwa kawai, shi ya auni jan digon daidai. Tunda ma, wurga mashi ne abinda yafi gwanacewa a ciki, bayan wurga duwatsu, kuma yawan ranakun yawo a daji ya bashi abubuwan aunawa dayawa. Ya saba da yasamu abubuwan da suka auna idanma yayunsa suka gagara.

Thor ya rufe idanunsa ya kuma ja numfashi. Idan bai samuba, masu tsaron fadan sarkin zasu dira a kansa su kaishi kurkuku---sai zarafin shiga runduna ya zama masa tarihi har abada. Wannan lokacin ke rike da mafarkunsa na tuntunda.

Ya roki Allah da duk abubuwanda yakedashi.

Batareda jinkiriba, Thor ya bude idanunsa, yayi taku biyu zuwa gaba, ya kwanta baya, ya wurga mashin.

Yarike numfashinsa a yayinda ya kalli mashin na tafiya a iska.

Mashin ya yanki shuru, mai kaurin, kuma Thor yaji darurukan idanun dake kallonsa.

Sai, bayan wani dadadden lokaci, sai ga wata kara, batantama karan mashi na huda ciyawa. Thor baima kalla ba. Ya sani, ya sanine kawai, awu ne daidai. Daga yanayin mashinne a lokacinda yabar hanunsa, lankwasan wuyan hanunsa, daya gaya masa cewa zai samu abin awun daidai.

Thor yayi kasadan kallo---ya gani, da babban sakewa, cewa gaskiya ne. mashin ya samu wuri a sakiyan jan digon—mashi kadai dake cikin wurin. Yayi abinda ya gagari shauran sabin dauka.

Shurun mamaki ya mamayeshi, ayayinda yan shauran sabin daukan---da gwanayen mayakan—duk suna masa kallon yan kauye.

Daga karshe, Kendrick ya maso gaba ya buga Thor a hankali a baya da tafin hanunsa, da karan gamsuwa. Yayi murmushi da fadi.

“Na yi gaskiya,” yace. “Zaka saya!”

“Me, ubangidana!” mai tsaron fadan sarki yayi ihu. “Wannan ba adalci bane! Wannan yaron ya iso ba gayyata!”

“Ya samu wannan abun awun. Wannan ma ishahsen gayyata ne a wuri na.”

“Yafi shauran rashin shekaru da kankanta da rata mai yawa. Wannan ba rundunan masu fisarin kwance bane,” janar din yace.

“Gwamma mani dan karamin mayaki da zai samu duk abinda ya auna da babban dolon da ba zai samu ba,” gwanin mayakin ya mayar.

“Wurgin sa’a!” yaronda suka tashi fada da Thor yayi ihu. “Inda muma zamu samu kari wasu zarafi, zamu sami abin awun, muma!”

Gwanin mayakin ya juyo ya kalli yaron da yayi ihun a kasa.

“Zaka iya?” ya tambaya. “Zan iya ganinka kayi a yanzu? Mu daura zamanka a nan a kan musun?”

Yaron, arikice, ya saukar da kansa a cikin kunya, azahiri baya son yayi musun.

“Amma wannan yaron bako ne,” janar yayi jayayya. “Bamu ma san inda ya fito ba.”

Duka shauran sun juya suga wanda yayi Magana, amma ba sai Thor ya juya ba---ya gane muryan. Muryanda ya damu yarantansa gaba daya ne. muryan babban wansa: Drake.

Drake yayiwo gaba da shauran yan’uwansa biyu, suna hararan Thor da kallon rashin yarda.

“Sunansa Thorgrin, dan zuriyan McCleod na gundumar kudancin masarautar gabas. Shine dan autan yara hudu. Duk mun fito gida daya ne. Yana kiwon tumakin mahaifinmu ne!”

Gabadaya tarin yara maza da gwanayen mayakan suka fashe da dariya.

Thor yaji fuskarsa yazama jazur; Kaman zai mutu a lokacin. Bai taba jin kunya Kaman haka ba. Yanayin dan’uwansa kenan, ya dinga karbe masa lokutan yabonsa, ya dinga yin duk abinda zai yiwu domin kaskantar dashi.

“Kiwon tumaki, yakeyi?” janar ya tambaya.

“To abokan gabanmu tabattace zasu kauce masa!” wani yaron yayi ihu.

Wani fashewa da dariyan ta taso, kunyanda Thor keji ya karu.

“Ya isa!” Kendrick yayi ihu, da karfi.

Ahankali, dariyan ya saya.

“Gwamma mani mai kiwon tumaki da zai saiti abin awu a ko da yaushe fiye da yawanciku—da suka iya dariya, amma kusan babu wani abinda kuka iya kuma banda shi,” Kendrick ya kara.

Da wannan, wani shuru ya sauko wa yara mazan, wadanda suka daina dariya.

Thor ya godewa Kendrick har abada. Ya sha alwashin mayarmasa ta duk hanyan da ya iya. Kodama mainene ya faru da Thor, wannan mutumi ya, akalla, mayar masa da mutuncinsa.

“Bakasanibane, yaro, cewa ba yanayin jarumi bane yayi gulman abokanensa ba—balle ma danginsa, jinin sa?” gwanin mayakin ya tambayi Drake.

Drake ya kalli kasa, arikice, daya daga cikin lokuta masu karanci da Thor yaganshi a wargaje.

Wani daga cikin yan’uwansa, Dross, ya maso gaba yayi tawaye: “Amma ba a ma zabi Thor ba. Mu aka zaba. Ya biyo mu nan ne kawai.

“Bana binku,” Thor ya nace, akarshe shima yayi Magana. “Nakasance anan domin runduna. Ba domin ku ba.”

Babu muhimmanci a dalilin kasancewarsa a ana,” janar din yace, da haushi, ya maso gaba. “Yana bata wa dukanmu lokaci. Hakane, wurgin mashinsa yayi kyau, amma duk da haka ba zai shiga cikinmu ba. Bashi da gwanin mayaki da zai saya masa, kuma ba mai rakiyanda zai hada kai dashi.”

“Zan hada kai dashi,” wani murya ya kirayo.

Thor ya juya, tare da shauran. Yayi mamakin ganin, a saye wasu taku dagashi, yaro mai daidai shekarunsa, wanda ainihin yayi kama dashi, sai dai da farin gashi da idanu masu kyalli da launin ganye, sanye da mafi kyawun kayan yakin yan sarauta: kullin tsarka a rufe da alamu masu launin malmo da bakake---wani dan dangin sarki.

“Ba zai yiwuba,” janar yace. “Dangin sarauta basu hada kai da talakawa.”

“Zan yi yadda na zaba,” yaron ya mayar. “Kuma nace Thorgrin zai zama abokin hadinkai na.”

“Koda mun yarda da haka,” general din yace, “Ba zai zama da wani amfani ba. Bashi da gwanin mayaki da zai saya masa.”

“Zan saya masa,” wani muryan ya zo.

Kowa ya juya zuwa daya gefen, sai wani dan karan mamaki ya taso a cikin shauran.

Thor ya juya yaga wani gwanin mayaki a kan doki, asanye da mafi kyawun, kayan mayaka mai kyalli kuma sanye da ireiren makamai a kan damararsa. Yana kyalli mai kyau---yayi Kaman kallon rana. Thor ya iya ganewa daga yanayinsa, da sayuwansa, da kuma su shaidan kan hulan yakinsa, cewa daban yake da shauran. Zakara ne.

Thor ya gane wannan gwanin mayakin. Ya sha ganin zanensa, kuma yaji labarin tarihinsa. Erec. Ya gagara yarda wannan na faruwa. Shine mafi haskawan gwanin mayaki a zoben gaba daya.

“Amma maigidana, kariga kanada wanda ka sayawa,” janar din yayi tawaye.

“To sai na yi su biyu,” Erec ya amsa, a murya mai zurfi, na ji da kansa.

Wani shurun mamaki ya mamaye taron.

“To babu shauran abin fada,” Kendrick yace. “Thorgrin nada mai saya masa da abokin taraya. Maganan ya kammalu. Yanzu shi dan runduna ne.”

“Amma ka manta dani!” mai tsaron fadan yayi ihu, ya maso gaba. “Wannan duk ba hujja bane akan cewa yaron ya daura hanu akan mai tsaron sarki, kuma dole amasa horo. Dole adalci ya samu!”

“Za ayi adalci.” Muryan Kendrick za iya yanka karfe. “Amma zai zama a ganin damana. Ba naka ba.”

Amma yallabai, dole asashi a maboya! Dole a yi misali dashi!”

“Idan ka cigaba da wannan bayaninka, to kaine zaka je maboya,” Kendrick ya gaya wa mai tsaron, yana hararansa zuwa kasa.

Daga karshe, mai tsaron ya hakura; ba a jindadin rai ba, ya juya ya tafi, fuska jazur, yana hararan Thor.

“To ya zama ka’ida,” Kendrick ya daga murya ya fada. “Barka da zuwa, Thorgrin, cikin rundunan mayakan sarki!”

Taron gwanayen mayakan da taron yara mazan suka yi wani ihu sai suka juya kowa ya wase, zuwaga horon da dama suke yi.

Jikin Thor yamutu da mamaki. Ya gagara yarda da abinda ke faruwa. Yanzu ya zama dan rundunan sarki. Abin Kaman mafarki ne.

Thor ya juya zuwaga Kendrick, yana jin godiya fiye da yadda zai taba iya fada. Bai taba samun wani a rayuwarsa ba daya damu dashi, wanda ya bar hanyansa domin kulawa dashi, ya kareshi. Yanayin yayi masa wani iri. Ya riga yaji kusanta ga wannan mutumin fiye da mahaifinsa ma.

“Bansan yadda zan gode maka ba,” Thor yace. “Ina da babban bashinka akaina.”

Kendrick yayi murmushi zuwa gareshi. “Sunana Kendrick. Zaka zo kasan sunan da kyau. Nine babban dan sarki. Naso muradinka. Zaka zama kari mai kyau ga wannan hadin.”

Kendrick ya juya ya tafi da sauri, yanayin haka, Elden, katon yaron da suka yi fada da Thor, ya wuce a gefensa.

“Ka kula da bayanka,” yaron yace. “Muna kwana a bariki daya dukanmu, kasani. Kuma karka zata koda na dan lokaci karami cewa ka tsira.

Yaron ya juya ya tafi yana buga kafafuwansa a kasa kafin Thor ya mayar da martini; yariga yasamu abokin gaba daya.

Ya fara tunanin me ke rike a boye masa a nan, sai dan autan sarki ya hanzarto zuwa gareshi.

“Karka damu dashi,” ya gaya wa Thor. “Ya cika neman fada. Suna na Reece.”

“Nagode maka,” Thor yace, ya miko hanunsa, “da ka zabeni a masayin abokin tarayanka. Bansan da mai zanyi ba inda ba ka yadda ba.”

“Ina murnan zaban duk wanda ya yaki wannan dabban,” Reece yace da farin ciki. “Wancan fadan mai kyau ne.”

“Kana wasane?” Thor ya tambaya, yana share bushahsen jinni daga fuskarsa yana kuma jin doron hancinsa na kumbura. “Ya kashe ni.”

“Amma baka hakura ba,” Reece yace. “Abin sha’awa. Da kowanne ne a cikin shauran da zai kwanta a kwance ne. Kuma wannan wurgin mashin ya kasance wani na bala’i. a ina ka koyi wurgi haka? Zamu kasance abokan tarayya iya rayuwa!” ya kalli Thor kallo mai ma’ana kafin ya sha hanu dashi. “Kuma abokanai, ma. Nima ina jin haka.

Yayinda Thor ya sha hanu dashi, ya gagara daina jin cewa shi yanayin abokin iya rai ne.

Kwassam, sai aka yimasa cakulikuli a gefe.

Ya juya yaga wani yaron day a girmeshi a saye a wurin, mai zanzana a fata da daguwar siririyar fuska.

“Nine Feithgold. Dangidan Erec. Kaine dangidansa na biyu a yanzu. Wanda hakan na nufin zaka dinga bin ummurnina. Kuma munada gasa nan da yan mintuna. Zaka saya haka kawaine bayan an mai dakai dangidan gwanin mayaki daya fi kowanne sanuwa a masarautan nan? Ka bini! Da sauri!”

Reece ya riga ya juya ya tafi. Thor ya juya yabi dangidan yayinda ya sallaka filin a guje. Baisan ina zasu je ba---amma bai damu ba. Yana wakan murna ne a ciki.

Ya ci nasara.

Yaş sınırı:
16+
Litres'teki yayın tarihi:
10 ekim 2019
Hacim:
292 s. 5 illüstrasyon
ISBN:
9781632912473
İndirme biçimi:
Serideki Birinci kitap "A Jeren Zoben Mai Sihiri"
Serinin tüm kitapları
Metin
Ortalama puan 5, 1 oylamaya göre
Metin
Ortalama puan 4,8, 6 oylamaya göre
Metin
Ortalama puan 4,8, 5 oylamaya göre
Metin
Ortalama puan 5, 1 oylamaya göre
Metin
Ortalama puan 5, 2 oylamaya göre
Metin
Ortalama puan 0, 0 oylamaya göre
Metin
Ortalama puan 0, 0 oylamaya göre
Metin
Ortalama puan 0, 0 oylamaya göre
Metin
Ortalama puan 0, 0 oylamaya göre
Metin
Ortalama puan 0, 0 oylamaya göre